PSG ta lallasa Real Madrid a wasan share fage

PSG ta lallasa Real Madrid a wasan share fage

Kungiyar Real Madrid wadda kuma ita ce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai a kakar wasan da ta gabata ta fara saka da bakin zare inda ta sha kashi wajen kungiyar Paris Saint Germain (PSG) wadda ita ce kuma zakarar kofin Ligue 1 na kasar Faransa.

PSG ta lallasa Real Madrid a wasan share fage
Yan wasan Real madrid

Nanitome Ikone ne dai ya fara zura kwallon kafin daga bisani wani sabon dan wasan PSG din da suka siyo Thomas Meunier ya kara zura sauran biyun a cikin mintuna 35 da kuma 40.

Ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma sai kungiyar Real Madrid din ta zura tata kwallon ta hannun dan wasan ta marcelo a wani bugun daga-kai-sai-mai-tsaron gida da ya buga bayan da Serge Aurier ya taba kwallon da hannu a cikin akwatin yadi 18.

Bayan an dawo hutun rabin lokacin ne dai kuma sai mai horar da Real Madrid din Zinedine Zidane ya canja duka yan wasan nasa wadan da kuma suka ci gaba da bugawa har aka tashi. Duk da cewar basu zura kwallo ba to kuma suma basu bari aka zura masu ba.

Kungiyar ta Real Madrid dai ta buga wasan nata ba tare da Cristiano Ronaldo, Gareth Bale, Luka Modric dama Tony Kroos ba saboda hutun da suke ci gaba dayi bayan gaba gasar cin kofin kasashen turai wadda akayi a kasar Faransa.

Yanzu dai kungiyar ta Real Madrid zata buga wasan ta na gaba ne da Chelsea a ranar Asabar mai zuwa a can kasar ta Amuruka a cigaba da gasar Intercontinental Champions Cup campaign.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel