Direbobi sun kashe jami'an FRSC 35 cikin shekara daya

Direbobi sun kashe jami'an FRSC 35 cikin shekara daya

-Rahottani sun nuna cewa kusan jami'an hukumar hana hadarin hanyoyi (FRSC) 35 aka kashe cikin shekarar da ta shige

-An yi wannan bayani ne a zauren majalisar dokoki ta jihar Neja

-Mai yiwuwa kuma wani jami'in ya rasa mazakutarsa

Direbobi sun kashe jami'an FRSC 35 cikin shekara daya

Babbar jami'ar hukumar hana hadarin hanyoyi (FRSC) ta jihar Neja Susan Ajenge ta bayyana cewa kusan jami'ansu 35 suka rasa rayukansu daga hannun direbobi a kan hanyoyin kasar cikin shekarar da ta wuce Ajenge ta bayyana haka a zauren majalisar jihar Neja, inda ta ce haka ya faru yayin da jami'an ke kokarin tsare dokokin hanya a kan manyan titunan kasar

Ta ci gaba da cewa, wani jami'in na can asibiti rai hannun Allah sanadiyar bankeshi da akayi kan aikinsa. Taci gaba sa cewa, jami'in na iya rasa mazakutarsa domin an yi masa tiyata har sau biyu.

KU KARANTA : Uwargidan Asari Dokubo ta rasu a hadarin mota

Daily Post ta ruwaito cewa majalisar jihar ce ta gayyato hukumar domin tayi bayani game da zargin da jama'a ke yi cewa jami'an hukumar na muzguna masu da sunan samo ma gwamnati kudaden shiga Yayin da take mai da martani, Ajenge ta kare hukumar, tana mai cewa maimakon jama'a su kiyaye dokokin hanya masu sauki, sun gwammace su juyo su soki da zargin hukumar

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel