Dan wasa Alexandre Pato ya koma Kungiyar Villareal

Dan wasa Alexandre Pato ya koma Kungiyar Villareal

 

– Dan wasa Pato ya koma Kasar Spain bayan ya dan taba wasa a Kasar Ingila.

– Paton a Kasar Brazil ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da Kungiyar.

– Alexandre Pato ya samu buga wasanni biyu kacal ne a Chelsea, inda ya ci kwalla daya.

Dan wasa Alexandre Pato ya koma Kungiyar Villareal

Tsohon dan wasan Chelsea Alexandre Pato ya bar Corinthians zuwa Villareal ta Kasar Spain. Zaman sa a Chelsea ya ci kwalla guda a wasan sa na farko da Aston Villa inda Chelsea ta ci 4-0.

Dan wasan Kasar Brazil, Alexandre Pato ya bar Kungiyar Corinthians da ke Brazil din zuwa Villareal da ke Spain. An dai kammala cinikin dan wasan zuwa Kungiyar Villareal din da ke La-liga. A baya kadan, dan wasa Pato yayi kokarin bugawa Kungiyar Chelsea, a matsayin dan wasan aro, hakan dai wani ci tura ba. Kulob din Corithians da ke Kasar Brazil ta fitar da wannan sanarwa, Kungiyar tana mai jawabi ta hannun darektan ta na kwallon kafa Edu Ferreira, cewa Dan wasan zai bar Kungiyar. Duk da dai Kungiyar ba ta bayyana asalin nawa aka kashe wajen sayen dan wasan ba, ana tunani Villareal din ta biya miliyan €3 ne wajen sayen dan wasan.

KU KARANTA: JUVENTUS TA SAYE HIGUAIN DAGA NAPOLI

Tsohon dan wasan AC Milan Pato mai shekaru 26 a duniya ya koma Corinthians ne a shekarar 2013, daga nan ya koma Kungiyar Sao Paulo aro na shekaru biyu, daga nan ne ya zarce Chelsea, har wa yau, aron na dan lokaci. A Chelsea dai dan wasan ya buga wasanni biyu ne kacal a zaman sa, ya kuma samu zura kwallo guda wasan san a farko a Premier League da Aston Villa. A Corinthians dan wasan ya buga wasanni 62 har ya ci kwallaye 17, a Sao Paulo kuma ya buga wasanni 101, ya kuma jefa kwallaye 38. Yanzu dai, ya zama dan Kungiyar Villareal.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel