Javi Martinez yayi magana kan Ancelotti Sabon Kocin Bayern

Javi Martinez yayi magana kan Ancelotti Sabon Kocin Bayern

 

– Dan wasa Javi Martinez yayi magana game da tattaunawar su da Ancelotti.

– Dan wasan ya kuma yi magana dangane da Pep Guardiola.

– Martinez ya tofa albarkacin bakin sa game da wasu batutuwan.

Javi Martinez yayi magana kan Ancelotti Sabon Kocin Bayern

 

 

 

 

Dan wasan tsakiya na Bayern Munich, Javi Martinez ya bayyana tattaunawar sa da sabon Kocin Kungiyar Carlo Ancelotti, a cewar Martinez, Sabon mai horaswar ya umarce da su rika buga wasan su kai tsaye. Dan wasa Javi Martinez ya lashe kofin Bundesliga har 3 a zamanin Koci Pep Guardiola. Sai dai sabon Kocin Kungiyar yana so su kara ma wasan na su sauri. Tuni dai aikin Carlo Ancelotti ya burge Javi Martinez. Dan wasa Martinez yace tun ranar fari Ancelotti ya burge su. Dan wasa Javi Martinez duk kusan halin su daya (Pep da Carlo) sai dai sun sha bambam wajen yanayin aikin su.

KU KARANTA: KYAFTIN DIN BAYERN YAYI MAGANA GAME DA SABON KOCI ANCELOTTI

Javi Martinez yace: “Koci Carlo (Ancelotti) yake tambaya ta game da inda zan buga, na bayyana masa ni abin da ke so kurum, in taimaki Bayern; ko ta wane hali zan iya. Bani damuwa da wai ina na buga, ko baya ko tsakiya ne… Saboda haka ni duk inda aka ce in buga, nan zan buga. Yanzu dai wajen horo ina buga baya, saboda babu ‘yan bayan, watakila idan an dawo gasa, in koma tsakiya. Ni dai zan iyaka nawa.” Dan wasa Martinez kuma yana ganin cewa za su iya cin kofuna karkashin Koci Ancelotti. Muna daga cikin wadanda suka fi kowa a duniya, burin mu ci duk wani kofi; Bundesliga, Super Cup, Champion league…a bara Atletico ta mana tsiya, amma mun fi su iya kwallo. Inji Martinez.

Martinez dai ya karyata rade-raden cewa zai bar Kungiyar, yace bai taba ma tunanin tashi ba. Ya bayyana cewa, Mario Goetze dai ya sanar da shi maganar tafiyar sa, kuma sai ga shi ya tashin, Martinez yace Dortmund din ya fi masa.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel