Gwamnati bata shirya tattaunawa ba - Neja DeltaAvengers

Gwamnati bata shirya tattaunawa ba - Neja DeltaAvengers

-Neja Delta Avengers sunce gwamnatin tarayya bata shirya ma tattaunawa ba

-Yan tsagerun na masu cewa jan jikin dabara ce ta samun lokacin sayen jiragen sama fasu sarrafa kansu

-Kungiyar suna gaya ma shugaba Buhari cewa Komi yawan jiragen sama ba zai hana su gurguntar da tattalin arzikin kasar ba

Gwamnati bata shirya tattaunawa ba - Neja DeltaAvengers

Tsagerun Neja Delta (NDA) sun zargi gwamnatin tarayya da munafurci game da tattaunawa da su, tana mai cewa gwamnatin ba da gaske take ba domin ta nuna kamar sune basu san tattaunawar

Mai magana da yawun kungiyar Mudoch Agbinibo, Ya ambaci haka ranar Talata, 26, ga Yuli. Yana mai cewa NDA ta sami bayanan sirri da ke cewa tattaunawar da gwamnatin tarayya ke magana yaudara ce kawai kafin jiragen sama masu sarrafa kansu da ta sawo daga Amurka su iso cikin watan Augusta.

KU KARANTA : Tsagerun MEND sun nunawa Buratai yatsa

Bayanin ya ci gaba da cewa "abin sai ya baka mamaki, ka tambayi Kanka wai wannan wace irin kasa ce? Muna ma gwamnatin shugaba Buhari kallon 'yar damfara. Ba da gaske take game da tattaunawa ba, tana haka ne domin a dauka  'yan Neja Delta Avengers ne basu shirya ma tattaunawa ba. Shugaba,kana iya saye duk jirage masu sarrafa kansu dake Turai da Amirka, wannan ba zai hana mu durkusar da tattalin arzikin Najeriya ba

"Barna mafi muni da zaka iya yi shine kasa sojoji su yi abin da suka kware kashe wadanda ba ruwan su, amma ka sani tattalin arzikin Najeriya zai raunana kuma ba zaka iya saida ko da lita daya ta danyen mai daga Neja Delta ba. Gara ka maida hankali wajen gano mai daga arewa maso gabas domin ko digo ba zaka iya saida wa ba daga kasarmu"

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel