Matasan APC, PDP sun mamaye majalisar dokoki

Matasan APC, PDP sun mamaye majalisar dokoki

-Jami’an tsaro sun hana matasa haddasa tashin hankali da karya doka a majalisar jihar Benue

-Shugaban majalisar ya dakatar da Kester Kyenge, na jam’iyyar PDP na tsawon watanni biyar bisa zargin mugun hali

Matasan APC, PDP sun mamaye majalisar dokoki
Gidan majalisar dattawan Najeriya

Ana rikici a majalisar jihar Benue kan motan milliyan 750 da aka siya da kudin zamba, rikicin ya kara rincabewa yayin da matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na jam’iyyar Peoples Democratic (PDP) suka mamaye majalisar a ranar Talata, 26 ga watan Yuli.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jami’an tsaro, wanda suka hada da Mobile Police Force da kuma jami’an Department of State Services (DSS), duk da haka, sai da suka tabbatar sun hana matasan haddasa fitina da karya doka a ciki da wajen majalisar.

Jami’an sun kuma saka kurin binciken ababen hawa sama da mita 800 daga majalisar, suha maganta duk wanda ya dauki hanyar majalisar.

KU KARANTA KUMA: Sanata Ali Ndume yayi Magana kan abubuwan da suka faru a majalisa

Mamayewar da matasan sukayi ya biyo bayan dakatarwan watanni biyar da jagoran majalisar ya ba Kester Kyenge, na jam’iyyar PDP a ranar Talata kan abunda ya kira da “ba halin shugabanci ba da kuma yin maganar kage ga shugaban majalisar da yunkurin bata sunan dukkanin yan majalisar.”

A cewar jaridar Daily Trust, domin mai da martani ga dakatarwan, shugaban yan tsirarun majalisar, Audu Sule, ya bayyana cewa ba’a ba Kyenge daman Magana ba kuma cewa an rushe dokar majalisa da ta bayar da daman a dakatar da mamba na tsawon kwanaki 14 kawai.

Ya bayyana dakatarwan a matsayi batattu.

Mu tuna cewa an samu tashin hankali a majalisar jihar Benue a ranar Talata 19 ga watan Yuli, yayin da aka fara binkice a tsakanin yan majalisa kan zargin zamban motan naira milliyan 750.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel