Batun komawar Dan wasa Pogba Man Utd, ina aka kwana?

Batun komawar Dan wasa Pogba Man Utd, ina aka kwana?

 

– Dillalin Paul Pogba ne ya sa maganar tafiyar Dan wasan zuwa Man Utd ta tsaya cak!

– Har an kai munzalin da Man Utd za ta duba lafiyar dan wasan, sai Mino Raiola ya kawo wani sabon labari.

– Kawo yanzu, za a ce Paul Pogba dan wasan Juventus ne.

Batun komawar Dan wasa Pogba Man Utd, ina aka kwana?

 

 

 

 

 

 

 

Kungiyar Man Utd sai ta kara hakuri kadan wajen sayen dan wasa Paul Pogba daga Juventus, Dillalin dan wasan tsakiyar Paul Pogba mai suna Mino Raiola ya soke maganar duba lafiyar dan wasan a Birnin Miami na Amerika. Har an kai Kungiyar Man Utd za ta auna lafiyar Dan wasan, ganin cewa ta kammala sayen Dan wasan, kwatsam sai dillalin na sa (Pogba) ya kawo wata sabuwa. Jaridu daga Spain sun rahoto cewa Mino Raiola, dillalin dan wasan ya tsaida maganar ne domin kuwa shi ba a gama maganar kudin sa ba.

KU KARANTA: TAFIYAR POGBA MANUTD, ME KE KAWO CIKAS NE?

Rahotanni sun bayyana cewa har an shirya cewa dan wasan mai shekaru 23 zai je wani asibitin kwararru da ke Miami domin duba a lafiyar sa, hakan zai sa a kammala cinikin na sa zuwa Man Utd. Dakta Italo Linfante ne wanda ya kamata ya auna lafiyar Dan wasan, sai dai Raiola wanda shi ne ke wakiltar dan wasan, ya sanar da Dakta Linfante cewa ka da ya sake ya dawo aiki a wannan lokaci, Dakta Linfanten dai yanzu haka yana Turai inda yake daukar hutu. Hakan dai zai sa a kara jan maganar har sai M. Raiola ya samua abin da ya ke nema.

Sabon Kocin Man Utd Jose Mourinho na neman tsohon dan wasan Kungiyar, Paul Pogba na Juventus. An dai amince da komai yanzu haka, abin da kawai ya rage shine a duba lafiyar dan wasan kafin a saye sa. Man Utd ta saye yan wasa da suka hada da; Zlatan Ibrahimovic da Henrikh Mkhitaryan. Ana sa ran Man Utd za ta saye tsohon dan wasan na ta, Paul Pogba kan kudin da ya kece na kowa a tarihin duniyar kwallo.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel