UBA ta bayyana gaskiya a kan al’amarin juyin mulki

UBA ta bayyana gaskiya a kan al’amarin juyin mulki

Bankin United Bank of Africa (UBA) tayi fashin baki akan rahotannin da ke jingina ta da daukar nauyin yunkurin juyin mulki a kasar Turkiyya .

A wata hira da yan jaridan da banki ta bayar da yamman ranan talata, ta musanta maganar da wata Jaridar kasan Turkiyya mai suna, Yenisafak,na cewa wasu daga cikin wanda gwamnatin Turkiyya ta damke  masu hannu a kaidin juyin mulkin a ranar 15 ga watan yuli, sun ce bankin ne ke daukan nauyin su.

UBA ta bayyana gaskiya a kan al’amarin juyin mulki

Game da rahotannin da aka samu da fari, abubuwan zargin sun ambaci sunan wani hafsan sojan Amurka, Janar John .F. Campbell a matsayin mai daukan nauyin su. An kara da cewan kudin da aka kashe a yankin kudi $2 biliyan wanda aka tura daga kasar Amurka zuwa bankin UBA kuma daga bankin masu juyin mulkin suka cire kudin.

Shugaban sadarwan bankin Charles Aigbe, ya fada a wata jawabi a ranar talata cewa bankin su bata san komai game da hakan ba.

KU KARANTA: Turkiyya: An kame mutane 10,410 a juyin mulki

“UBA na sane da maganganun da akeyi a kafafun yada labarai na jingina bankin mu da abnda ya faru a kasar turkiyya kwanan nan. Saboda haka muna san mu bayyana cewa UBA ba tada hannu a cikin tuhume-tuhumen da ake yi,duk wani magana da akeyi karya ne ,babu gaskiya a ciki. Zamu cigaba da mayar da hankali domin karfafa babban bankin nahiyar Afrika,.

Asali: Legit.ng

Online view pixel