EFCC ta cafke wani shugaba a APC

EFCC ta cafke wani shugaba a APC

Hukumar yaki da zamba da yiwa tattalin arzikin kasa zaman kasa EFCC ta cafke tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai Cif Chibudom Nwuche da laifin badakalar kwangila na tsabar kudi naira biliyan 5 da miliyan 600.

EFCC ta cafke wani shugaba a APC
Nwuche

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, EFCC ta cafke Nwuche ne bayan ya amsa gayyatan da tayi mai a ranar Litinin 25 ga watan yulio. Kama shin na da nasaba da badakalar kwangilar da aka bankado daga ofishin yin afuwa gay an ta’adda.

 

Jami’an hukuman EFCC sun ce akwai sa hannun Nwuche a cikin badakalar kudi naira biliyan 2 da miliyan dari takwas da Kingsley Kuku ya sata da sunan tura tsaffin tsagerun Neja Delta karatu kasashen waje a shekarar 2012.

EFCC ta cafke wani shugaba a APC

Wata majiya dake hukumar ta gultmata mana cewa:”ana binciken Nwuche ne dangane da badakalan sace kudi naira biliyan 5 da miliyan 600 da kamfaninsa mai suna Foundation for youth Development ta amsa daga ofishin kula da tubabbun tsagerun Neja Delta wadda Kingsley Kuku ke shugabanta. “ ana zargin an bashi kwangila daga ofishin kula da tubabbun tsagerun Neja Delta a shekarar 2012 don yi musu horo a kasar Malaysia. Amma har zuwa lokacinnan, ba’a aiwatar da kwangilan ba, kuma ya amshi kudin naira biliyan 2 da miliyan 800.”

Kamar yadda jami’in ya fada, an saci kudin ne ta wasu kamfanunuwa, mutane da wuraren canjin kudi kuma aka mika ma Kuku kudin ta hanyar wani mutum da ya tsaya a madadinsa wanda shima ana bincikansa. Har zuwa karfe 8 na yammacin ranar Litinin ana binciken Nwuche. Nwuche ya taba kasancewa dan majalisa a majalisar wakilai ta kasa a tsakanin 1999 zuwa 2003 a karkashin jam’iyar PDP.

Nwuche ya taba kasancewa mataimakin shugaban jam’iyar PDP a zamanin Bamanga Tukur, kafin daga bisani ya watsar da PDP ya rungumi APC bayan shugaba Buhari ya lashe zaben Shugaban kasa na 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel