Yan bindigan Neja Delta sun kai farmaki Jihar Legas

Yan bindigan Neja Delta sun kai farmaki Jihar Legas

–Rahotanni da dama sun tabbatar da cewan yan bindiga sun kai hari wata unguwa suka bude musu wuta,suna kasha mutane.

–Yan sanda sun fita ceton mutane da gaggawa ta hanyar tare hanyoyin da yan bindigan zasu iya fice wa.

An samu wani tashin-tashina da safiyar ranar talata, 26 ga watan yuli a unguwar Ewedogbon da ke garin Igando da ke Jihar Legas yayinda yan bindigan Neja Delta suka kai farmaki unguwar. Rahotanni da dama sun tabbatar da cewan an rasa rayuka da dama sanadiyar shiga gidajen mutane da yan bindigan keyi suna kashe su. Amma har yanzu ba’a san yawan mutanen da suka rasa rayukan suba a lokacin bayar da wanna rahoton.

Yan bindigan Neja Delta sun kai farmaki Jihar Legas
Niger Delta Avengers

Mazaunan unguwan sun bayyana cewa ayarin yan bindigan sin zo ne sassafe rike da manyan bindigogi da wasu muggan makamai. Wani mazauni da bai son a ambaci sunansa yace yan bindigan sun shigo ne suka fara ruwan harsasai. Ya tura sako kafar sada zumunta ta Whatsapp, yace:

“Ku taimaka ku kira mana layin gaggawa yanzu unguwar Ewedogbo ,LASU road. Yan bindigan Neja Delta na kasha mutane a yanzu haka, babu wanda zai iya shiga ko fita, ni idon shaida ne, dan Allah,ku taimaka ku yada wannan labari,” . Yace babu wanda ke iya fitowa daga gidajen su saboda yan bindigan na shiga gidajen mutane .

An samu cewa wasu Jami’an yan sanda sun zo da gaggawa amma yan bindigan sun riga sunyi aika-aika a lokacin,sun arce. Kakakin jami’an yan sandan Jihar Legas yace jami’an yan sanda nada masaniya akan farmakin kuma ta tura ayarin yan sanda domin cecen rayuwan mutane da dukiyoyin su.

KU KARANTA : Wani mai gida ya hallaka dan haya a Lagos

Jihar Legas dai ta zama gidan kasha-kashe da garkuwa da mutane . A lokuta daban daban , yan bindiga sun kai hare-hare unguwanni a Ikorodu da Igando,kuma duk da makudan kudin da gwamnan jihar, , Akinwunmi Ambode, ke zubawa a bangaren tsaron jihar.

A ranar lahadi, 24 ga watan yuli, yan bindiga sunyi garkuwa da wani faston cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ke tashan Santos a Isawo,Ikorodu, jihar Legas. Kuma wannan ya faru ne kimanin mako 1 bayan anyi garkuwa da wani sarkin gargajiya a Legas.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel