Wani mai gida ya hallaka dan haya a Lagos

Wani mai gida ya hallaka dan haya a Lagos

-Wani mai gidan haya ya yi ajalin wani dan hayan gidansa

-‘Yan sanda sun damke wanda ake zargi

-Mai gida ya aikata kisan ne bayan wata doguwar takaddama

Wani mai gida ya hallaka dan haya a Lagos
Wasu unguwannin da ke jihar Lagos

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ya damke wani mai gidan haya Gbade Metibemu a bisa zargin ya hallaka wani dan haya a yankin Makoko da ke jihar Legas.

A cewar jaridar Punch, Mista Metibemu ya soki marigayin ne Abraham da wuka, bayan da ya ki tashi daga gidan da ya ke haya na watannin hudu, bayan da suka kai kimanin mako guda suna takaddama, a cewar wani wanda ya gani da idonsa, wanda ya kuma kara da cewa, mai gidan ya gargade shi  da ya daina bata wurin da kashin ‘yar sa.

KU KARANTA: Boka ya kashe wani mutum bayan ya damfare shi

Ganin cewa gargadin da ya ke yi ba ya shiga kunnen dan hayan ne, a cewar majiyar, sai mai gida Metibemu ya yi barazanar hallaka shi, hakan kuwa ya kasance a ranar Alhamis  21 ga watan Yuli da misalin karfe 10:00 na dare, a lokacin da ya ke shirin kwanciyar barci sai fada ya barke tsakaninsu da mai gida a inda ya kuma ya soke shi da wuka.

Bayan ya garzaya ofishin ‘yan sanda a inda ya kai karar cewa dan hayarsa ya ji mi shi ciwo ne, sai reshe ya juye da mujiya, yayin da ya ‘yan sanda suka samu labarin mutuwar dan haya a asibitin da ka kai shi.

Wani Jami’in ‘yan sanda Dolapo Badmus, ya tabatar da aukuwar lamarin, ya kuma ce an mika wanda ake zargi bangaren ‘yan sanda masu binciken aikata manyan laifuka da ke Yaba.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel