Tashin hankali a Abuja yayinda yan fashi suka zo Banki

Tashin hankali a Abuja yayinda yan fashi suka zo Banki

– Wata tawagar yan fashi sun far ma wani mutumi kudi N4.3miliyan a gaban bankin Access Bank.

– Jami'an tsaron bankin sunyi musayar wuta da yan fashin yayinda mutane suka baje domin kare rayukansu.

Tashin hankali a Abuja yayinda yan fashi suka zo Banki

Hankalin mutane ya tashi a garin Kubwa, inda wata gangamin yan fashi suka far ma wani kwastoman Access Bank suka kwace masa kudi N4.3 miliyan da safiyar litinin.

Game dani idon shaida, Jubril Mohammed, yace yan fashin sun biyo mutumin ne daga wata gidan mai inda mutumin ke aiki kafin suka  kwace kudin.

Wani dan sandan bankin yayi musayar wuta da su. Mutumin yazo ajiye kudin a asusun sa ne Amma suka dauke kudin. Amma, mutumin ba samu rauni ba, mutum daya ne kawai ta samu rauni a lokacin da ake musayar wuta. Wani ma'aikacin kamfanin etisalat da ke da ofishi a gaban bankin.

Tashin hankali a Abuja yayinda yan fashi suka zo Banki
Photo credit: Sahara Reporters

Mr. Mohammed yace : “Ina tsaye a nan kawai sai naga wata mota ta zo da gudu gaban bankin ,sai mutane 4 suka fito da bindigan su suka fara harbin motan mutumin. Daya daga cikin su ya bude wurin ake ajiye kaya na motan ya dauki jaka cike da kudi.”

KU KARANTA : Hmmn! Wata ‘yar coci ta aika wata lahira

Jami'an yan sandan da suka zo wurin sun dauki motan mutumin da kuma kayan makaman da yan fashin sukayi amfani dashi. Harkokin kasuwanci suka tsaya cak . munyi yunkurin sauraron magana daga bakin manajan bankin ko jami'an yan sanda, amma suka kiya.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel