Nnamdi Kanu ya ce Allah ne ya yanke hukuncin neman Biyafara

Nnamdi Kanu ya ce Allah ne ya yanke hukuncin neman Biyafara

-Nnamdi Kanu shugaban kungiyar Indigenous People of Biafara  (IPOB) yayi magana daga gidan Yari

-Daraktan Radiyon Biafra yace neman Biyafara ba shawarar sa bane amma kiran na Allah ne

-Ya ce yunkurin tabbatar da Biyafara abune da baza’a iya daina wa ba

Shugaban Radiyon Biyafara, Nnamdi Kanu yayi Magana daga gidan kaso a ranar Litinin 25 ga watan Yuli, ya yi ikirarin cewa ba yin sa bane ya zabi neman Biyafara ba, amma kira ne da Allah yayi.

Nnamdi Kanu ya ce Allah ne ya yanke hukuncin neman Biyafara

Shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke tsare, ya nace kan cewa shawarar da ya yanke na mayar da kasar Biyafara ba zabin kansa bane amma umarni ne daga Allah madaukaki (Chiukwu-okike-abiama), wanda aka sanya shi tun da dadewa.

Sakataran labaran kungiyar IPOB, Comrade Emma Powerful wanda ya bayyana hakan a jiya a wata sanarwa, yace Kanu ya bayyana wa wasu masu tausaya masa da suka ziyarce shi a kurkuku cewa ya sadaukar da rayuwarsa don gannin ya dawo da Biyafara, kamar yanda Ubangijinmu Yesu Almasihu (Lord Jesus Christ) ya sadaukar da rayuwar sa domin ceto yan’adam.

KU KARANTA KUMA: Jonathan tare da iyalin sa a filin jirgin sama na Abuja (hotuna)

Yayi tambaya: “Ta yaya zan karfafa wa mutanen Biyafara gwiwa kan suyi aiki gurin ganin sun kawo ci gaba a kasar Najriya, alhalin bama jin yare daya, bama cin abinci daya kuma al’adun mu ba daya ba.

Idan muka je kasarsu domin aikata al’adunmu da addininmu, za’a fille mana kai. Matansu suna sanya hijab, matan Biyafara basa sanya wa,saboda haka idan suka ga cewa matanmu basa sanya hijab, kuma bama addini guda, zasu dauke mu a matsayin bare sannan zasu fille mana kai. Mun kasance Kiristoci dari bisa dari. Mutanen nan Musulmai ne da suka dauki kisa a matsayin al’ada.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mazi Kanu ya bayyana cewa “babu danasani a rayyuwarsa,” ya kara da cewa “a shirye yake yayi shekaru dubu a gidan yari”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel