An sace wa Kocin Najeriya Samson Siasia, Kudi a Amerika

An sace wa Kocin Najeriya Samson Siasia, Kudi a Amerika

 

– Yan fashi sun far ma Kocin yan kwallon Najeriya.

– Barayin dai sun fasa masa mota ne.

– Samson Siasia bai sanar da kowa wannan batu ba.

An sace wa Kocin Najeriya Samson Siasia, Kudi a Amerika

 

 

 

 

 

 

Kocin Kungiyar Najeriya ta Olympics, Samson Siasia ya hadu da sharrin masu dan hali a Kasar Amerika. An yi wa Kocin na Kasar Najeriya da mataimakin sa sata a Birnin Atlanta Georgia na Kasar Amerika. An dai shiga cikin motar ta Samson Siasia ne aka dauki wasu kayayyaki. Barawon da yayi wannan aiki, ya fasa motar Kocin ne da ke ajiye a gaban otel din da ‘yan Kasar Najeriya su ka sauka, inda ya saci katin ‘Credit Card’, Kudi, da kuma wayoyin salula. Jaridar Sporting Life ta rahoto wannan labari. Sai dai kocin yayi kokarin yin shiru ba tare da an san maganar ba, hakan zai sa ya fi maida hankali wajen horas da ‘yan wasan sa masu shirin buga Gasar Olympics da za a yi a Rio na Kasar Brazil nan da mako biyu.

KU KARANTA: SHUGABAN KUNGIYAR FIFA TA DUNIYA YA ISO NAJERIYA

Bayan da Kocin Najeriya Samson Siasia ya tafi aikin horar da yan wasa da yammaci, ko da ya dawo, bayan ya kintsa, sai ya lura cewa an yi masa sata a mota. An balle kofar motar ne aka sace masa katin ‘Credit Card’, da wayoyin sa kirar Android har biyu, har ma da ta mataimakin sa. Da kuma kudi. Samson Siasia bai ji dadin ganin wannan abu ba, sai dai duk da haka, wannan bai ko say a gaza ba, tuni ya mike yace ‘Ba mutum ba, sai Ubangiji!’ babu abin da zai hana sa aikin da ya kawo shi, na shirya ma Gasar Olympics, Majiyar mu ta bayyana.

Da wani dan jarida ya tambayi Samson Siasia game da satar, sai yake cewa: “Kai wa ya fada maka? Ina ka samu labari?” Koci Samson Siasia sai ya bayyana cewa, Eh, da gaske ne, an yi masa sata. Amma wannan baa bin damuwa ba ne.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel