Arsenal ta jinjinawa ‘gwarzo’ Alex Iwobi na Najeriya

Arsenal ta jinjinawa ‘gwarzo’ Alex Iwobi na Najeriya

 

– Kungiyar ta Arsenal ta ce dan wasan na Kasar Najeriya, Tauraro ne.

– An tuna baya: Dan wasan ya ci kwallon san a farko ne a wani wasa da Arsenal din ta dagargaza Lyon da ci 6-0.

– Arsenal ta bayyana cewa dan wasan gaban na Kasar Najeriya, Alex Iwobi Gwarzo ne.

Arsenal ta jinjinawa ‘gwarzo’ Alex Iwobi na Najeriya

 

 

 

 

 

 

Dan wasan Arsenal mai shekaru 20 da haihuwa ya bayyana sunan sa a duniya a ranar 25 ga watan Yulin 2015, a ranar dai dan wasan ya taka rawar gani ne a wani wasa da Arsenal ta buga da Lyon a gasar cin kofin kawance na Emirates Cup. A ranar dan wasan ya burge kowa, har ya jefa kwallo a raga. Cikin minti tara kacal, Arsenal din ta durawa Lyon kwallaye hudu tun a zangon farko, da dai aka tashi wasan, Arsenal tayi kaca-kaca da Lyon din da ci har shidda da nema. An buga wannan wasa ne a shekarar bara, a wani gasar cin kofin da aka sani da Emirates Cup.

KU KARANTA: ZA NI GAISA DA PEP GUARDIOLA INJI JOSE MOURINHO

Olivier Giroud ya fara buda raga a minti na 29, kafin Alex Oxlade-Chamberlain, Aaron ramsey da kuma dan kasar Najeriya Alex Iwobi su kara duk a cikin ‘yan mintuna kadan. Da aka dawo hutun rabin lokaci kuma, dan wasa Oezil Mesut ya kara ta biyar, sai daga karshe Santi Cazorla ya aika wata bugun ‘firinkit’ har raga daf da a tashi. A jiya ne aka cika shekara guda da buga wannan wasa, Kungiyar Arsenal din ta fitar da bidiyo da lambar Alex Iwobi, da take mai ma’anar cewa ‘Bara war haka, aka gano Alex Iwobi!’ Arsene Wenger, wanda shine Kocin Kungiyar yana cewa: “Ina son halayyar sa da kuma wasan sa…” a ranar da aka buga wannan wasa. Wenger yace: “Ya (Alex Iwobi) yana da sauri, kuma yana gane wasa. Kuma yana da karfi, sannan ya san raga.”

Tun daga nan dai Alex Iwobi ya shiga idanun kowa a duniya, ya buga wasan san a farko na Premier a watan Oktoba na 2015, sannan ya buga wasan FA tsakanin su Sunderland. Ya kuma fara buga wasan san a UEFA Champions league na farko da Barcelona.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel