Mikel zai hade da tawagar Najeriya a Amuruka

Mikel zai hade da tawagar Najeriya a Amuruka

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea John Obi Mikel ya bar kungiyar tasa don ya hade da tawagar kasar Najeriya na Super Eagles da sukayi sansani a jihar Atlanta Georgia a kasar Amuruka.

Dan wasan dai Mikel ya bayyan hakan ne a shafin sa na sada zumunta na Instagram (@John_mikel_obi) A bayanin dai na shafin nasa Obi ya wallafa hoton sa ne da  kungiyar sa ta Chelsea inda yace: "mun kammala atisayen mu na farko yanzu kuma zan wuce Atlanta don haduwa da tawagar kasata Najeriya da zummar tafiyarmu gasar Olympics 2016."

Haka ma dai wani jami'in hukumar kula da harkokin kwallon kafar ta kasar Najeriya din watau Nigeria Football Federation (NFF) ya bayyana cewa John Mikel Obi tare da wasu su 4 duk zasu hadu da tawagar super eagles din a sansanin su na Atlanta.

Sauran Yan wasan da zahu hadu da tawagar sune William Troost-Ekong, Kingsley Madu, Oghenekaro Etebo da kuma Daniel Akpeyi. Ana dai sa ran Mikel din tare da sauran yan wasan duka zasu buga wasan kungiyar na karshe na shirye-shirye da kasar Hondurasa wadda itama zata buga wasan a gobe Talata 26 ga wannan watan.

Jami'in na hukumar NFF wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya kuma shaida mana cewa: "tabbas Mikel din tare da sauran 'yan wasan su hudu sun isa sansanin yan Super Eagles din a Atlanta" Ya kara da cewa: "Tabbasa zuwan nasu zai kara ma yan tawagar kuzari."

Su dai tawagar ta Super Eagles zasu kara ne a rukunin B tare da kasashen Sweden, Colombia da kuma Japan. Zasu fara bugawa ne kuma da kasar Japan a 5 ga watan Agusta mai kamawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel