An hana yan wasan Juventus tattauna batun tafiyan Pogba Man Utd

An hana yan wasan Juventus tattauna batun tafiyan Pogba Man Utd

A kokarinsa na ganin yan wasansa sun fuskanci sana’arsu, kocin kungiyar kwallon kafa ta Juventus Massimiliano Allegri ya haramta musu tattauna zancen yiwuwan tafiyan shahararren dan wasan kungiyar Paul Pogba zuwa Manchester United.

An hana yan wasan Juventus tattauna batun tafiyan Pogba Man Utd
Paul Pogba

Jaridar Mirror UK ta ruwaito ana tsammanin kungiyar Manchester United zata sayi dan wasan tsakiya akan makudan kudi bayan sun daidaita zancen albashinsa da shi kan pan 250,000 kowani sati. A shekarun baya ne dai Manchester ta siyar da Pogba akan pan 800,000.

 

Allegri ya haramta tattauna batun ne ganin cewa babu wata yarjejeniya da aka cimma a tsakanin hukumomin kungiyoyin biyu.

An hana yan wasan Juventus tattauna batun tafiyan Pogba Man Utd
Allegri-Kocin Juventus

“ba zan ce komai ba akan siya da siyarwan yan wasa ba, munzo nan ne kawai don atisaye,” inji Allegri a yayin da suke yawon atisaye a kasar Australia inda zasu fuskanci Tottenham a ranar talata. “hukumar kungiyar zata yi bayani dangane da siya da siyarwan, kuma suna kokari a wannan fannin, nayi murna da haka.” Sai dai kuma shi Pogba a yanzu haka yana hutu a Miami biyo bayan kaiwa ga wasan karshe da suka yi na gasan cin kofin nahiyar turai na 2016.

 

Sa’annan kuma, an dage wasa tsakanin Manchester United da Manchester City da za’a buga yau saboda lalacewar yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel