A rika sara ana duban bakin gatari – Sanata Ali Ndume

A rika sara ana duban bakin gatari – Sanata Ali Ndume

-Sanata Ndume ya bayyana ra’ayinsa dangane da abin da ya faru a majalisar wakilai

-Abin da ya faru bai kamata ba

A rika sara ana duban bakin gatari  –Sanata Ali Ndume
Ali Ndume

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai Sanata Ali Ndume, ya yi Allah Wadai da cece-ku-cen da ake yi kan aringizon da aka yi a kasafin kudin kasar.

Shugaban ya bayyana ra’ayinsa ne a wani taro da ya yi da ‘yan jarida a majalisar kasa, a yayin ya ke amsa tambayoyin ‘yan jarida kan cewa ko da akwai hannun majalisar dattijai a aikata abin kunyar.

Ndume ya ce aikin majalisa ne ta yi duban tsaf kan kasafin kudi da zaran an kawo mata, wanda hakan na sa alkaluman lissafi su canza, sannan ya kara da cewa, babu wani abu wai shi aringizo, “idan majalisa ta na aiki akan kasafin kudi, wannan ba aringizo ba ne...  aringizo abin Allah wadai ne,  bai dai kamta mu rika yi wa juna tonon silili a bainar jama’a ba”.

Rahotanni na cewa shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, shi da wasu shugabannin majalisar su uku suka yi aringizo a kasafin kudin shekara 2016 wanda shugaban kasa ya gabatar wa da majalisun biyu.

Wannan tonon silili ya biyo bayan da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya sauke Abdulmumini Jibrin kofa ne a matsayin shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, a bisa zargin karkatar da wasu ayyuka na biliyoyin nairori zuwa mazabarsa a jhar Kano, shi kuma ya mayar da martani da zargin cewa shugaban majalisar ne da wasu suka tilasta shi yin aringizon aiki ga mazabar shugaban majalisar.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel