Babban burin Neymar a rayuwa

Babban burin Neymar a rayuwa

Shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Brazil mai buga ma kungiyar kwallon kafa ta Bercelona wato Neymar ya bayyana burinsa na ganin ya zura kwallon da zata basu nasara a wasan karshe na gasan Olimfik da za’a buga kasar su ta Brazil.

Babban burin Neymar a rayuwa
Neymar

Brazil na yunwan lashe wannan gasan saboda shine kadai gasar da basu taba lashewa ba a tarihinsu. Don haka ne tun yanzu Neymar ya ci burin buga wasa a filin wasa na Maracana inda za’a fafata wasan karshe na gasar don lashe kyautan zinari a ranar 20 na watan Agusta.

 

Neymar yace “ina fatan idan muka je Maracana in zura kwallon da zai bamu nasara, ko in baiwa wani kwallo ya ci, ko kuma ma dai duk yadda ta kasance dai, mu zamu zamo zakarun,” ya cigaba da fadi “mun samu babban dama don mu kafa tarihi , mu ciyo ma kasar mu Brazil kyautar zinari.”

Babban burin Neymar a rayuwa
Neymar tare da yan kwallon Brazil

Neymar dan shekara 24 ya tuna karawar da suka yi a gasan Olimfik da aka yi a Landan a shekarar 2012 inda Brazil ta sha kasha a hannun Mexico a wasan karshe. Yace “Naji dadi na taba cin kyauta a gasar Olimfik, mun lashe kyautan azurfa a wasan karshe, muna fatan mu lashe kyautan zinariya a wannan lokacin”

 

A wannan lokacin kuwa su Neymar a gida zasu yi wasan tunda dai Brazil ce mai masaukin gasan, don haka zasu samu alfarma iri iri wajen neman lashe kyautan zinariya. Kungiyar Barcelona ta baiwa Neymar daman ya wakilci kasarsa Brazil a gasan Rio din, inda suke tsammanin ya dawo kafin karshen watan agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel