Yan bindiga sunyi garkuwa da Faston RCCG a Jihar Legas

Yan bindiga sunyi garkuwa da Faston RCCG a Jihar Legas

– Anyi garkuwa da wani faston kungiyarRedeemed Christian Church of God a yayinda suke bauta a jihar Legas

– Shugabannin cocin sun ce bazasu amince da cigaba da yin garkuwa da fastocinsu ko mambobinsu ba.

A ranar lahadi ne, 24 ga watan yuli yan bindiga sukayi garkuwa da faston cocin Redeemed Christian Church of God da ke Santos Bus Stop,Isawo,Okorodu da ke Jihar Legas.  Game da rahotanni, anyi garkuwa da faston mai suna Bajomo ne misalin karfe 7 na safe yayinda yake shirya ma ganawan ma'aikata. Wata idon shaida mai suna Esther, ta ce yan bindigan sun sanya kyawawan tufa kai kace ibada suka zo yi.

Yan bindiga sunyi garkuwa da Faston RCCG a Jihar Legas
Pastor Adeboye

“Faston yayi sammako misalin karfe 7 domin ganawar ma'aikata. Abun tsoron shine mutanen sin shigo a hankali kaman sabbin mambobi. Suna sanye da tufa kaman sun zo bauta Coci. Sun rike littafi ma a hannunsu. Ba su fito da kowani makami ba kuma basu harbi kowa na. Sai da suka kai wurin faston ne suka fito da makamai su kace ya biyo su. Faston ya je cocin kafin kowa, kuma mambobi 3 kawai suke nan lokacin da aka yi Garkuwa da shi.

“Sun tafi da faston mu. Wasu mambobin mu sun je gidan faston sun sanar da iyalansa. Abun takaici ne a ce a unguwar mu ana garkuwa da mutane, ana fyade, har kashe mutane kulli yaumin. Wannan babban matsala ne. Gaskiya ya kamata gwamnatin Jihar da jami'an yan sanda su dau mataki akan wannan abun da ya zama ruwan dare. Wadannan yaran Ijaw sun fitine mu.

KU KARANTA : Musulunci ya samu karuwa da wani Fasto (duba hotuna)

Shugaban kwamitin yada labarai na cocin, Fasto Segun Adegbiji, ya tabbatar da labarin. Har yanzu jami'an yan sanda basu tabbatar da labarin ba. Yace:

“Cocin Redeemed Christian Church of God bazata amince da cigaba da yin garkuwa da kisan fastocinmu da mambobinmu ba. Muna gargadi ga wadannan makasan kuma masu garkuwa da mutane cewan Ubangiji zai saukar musu da fushi.

A Bangare guda, matan nan mai wa'azin Redeemed Christian Church of God da aka kashe , Fasto Eunice Olawale, ta shiga kasa a makabartan gudu da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel