Ni zan karbi Shugaban Kungiyar FIFA-Chris Giwa

Ni zan karbi Shugaban Kungiyar FIFA-Chris Giwa

– Chris Giwa yace bai yarda ba, shi ne Shugaban Hukumar NFF na ainihi.

– Ana tsammanin zuwan Shugaban FIFA Gianni Infantino, ranar Lahadi 24 ga Watan Yuli.

 

Ni zan karbi Shugaban Kungiyar FIFA-Chris Giwa

 

 

 

 

Chris Giwa, mai Kungiyar nan ta Giwa FC da aka kora daga Gasar N.P.L, ya sha alwashin cewa shine ba wani ba, zai karbi bakuncin Shugaban Kungiyar FIFA ta Kwallon Kafar duniya idan ya zo Najeriya. Chris Giwa ya bayyana cewa shine zai je filin jirgin sama na Nmandi Azikiwe, wanda ta nan ne Shugaba Gianni Infantino na FIFA zai sauka a maraicen Lahadi 24 ga wannan Wata. Da alamu dai cewa akwai tsabar rikici a kasa, bayan da Amaju Pinnick ya gama shirya yadda za a karbi Shugaban FIFA da tawagar sa, sai ga Chris Giwa yana bayyana cewa ai shi ne zai karbi bakuncin Shugaban Gianni Infantino.

KU KARANTA: KYAFTIN DIN JAMUS ZAI BAR MAN UTD

Da shi (Chris Giwa)n yake tattaunawa da Legit.ng a ranar Lahadi 24 ga watan Yuli, ya bayyana cewa shine ainihin Shugaban Huukumar Kwallon Kafar Kasar ta NFF, kuma don haka ya shirya duk abin da ake bukata na tarbar Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa na Duniya da kuma Sakatariyar sa Fatima Samoura. Chris Giwa dai ya bayyana cewa shi kotu ta amince a matsayin Shugaban NFF a hukuncin da aka zartar na 8 ga watan Afrilun 2016. Chris Giwa yak e cewa: “Muna farin ciki da Shugaban FIFA ta duniya zai ziyarci Najeriya, na kuma shirya da tawaga ta, yarda za mu tarbe sa a filin jirgi idan ya iso”. Chris Giwa yace: “Ni ne Shugaban NFF, kuma wannan aiki na ne, saboda haka babu wanda ya isa ya hana ni aiki na

Ana dai ta sa-in-sa tsakanin Amaju Pinnick da Chris Giwa ga kujerar ta NFF, sai dai Amaju Pinnick ya shekara har biyu bisa kujerar Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kasar, kuma shi Kungiyar Kwallon Kafa ta Nahiyar (CAF) ta sani a matsayin Shugaba.

 

Source: Legit

Online view pixel