Wani tsohon Dan wasan Chelsea zai dawo Kungiyar

Wani tsohon Dan wasan Chelsea zai dawo Kungiyar

 

– Romelu lukaku na shirin barin Kungiyar Everton.

– Ronald Koeman zai saki dan wasan kan makudan kudi miliyan £75.

– Shi dai Antonio Conte na Chelsea bai ce komi ba game da batun.

Wani tsohon Dan wasan Chelsea zai dawo Kungiyar
Lukaku Romelu

Da alamun cewa Dan wasan gaba na Kungiyar Everton, Romelu Lukaku na iya komowa tsohon kulob din sa na Chelsea, don kuwa dan wasan na shirin barin Gidan Goodison Park na Kungiyar Everton. Dan wasan na Kasar Belgium ya sanar da abokan sa cewa yana da bukatar komawa Kungiyar Chelsea da ke London, ana tunani kwanan nan, dan wasa zai koma tsohuwar Kungiyar sa. Yanzu haka dai, Kocin na Kungiyar Everton na neman ‘yan wasan gaba a kasuwa, ganin cewa zai iya samun kudi har fam miliyan £75 idan ya saida dan wasa Lukaku Romelu.

KU KARANTA: BASTIAN SCHEWEINSTEIGER ZAI BAR MAN UTD

Da alamu dai Kocin na Everton ya hakura da tafiyar babban dan wasan nasa Lukaku mai shekara 23, ana tunani har ya fara neman wasu yan wasan da za sum aye gurbin sa, daya daga cikin su shine dan wasan Stoke City, Marko Aenautovic. Da alamu dai cewa dan wasan Kungiyar Stoke City din Marko Aenautovic, ba zai kara wani sabon kwantiragi ba da Kungiyar ta Stoke, hakan ke nuna cewa yana iya barin gidan Bet365 din na Stoke zuwa Goodison Park na Everton idan har aka saki kudin da ya dace.

A SAUKE MANHAJAR MU Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

Sai dai har yanzu Kocin Kungiyar Chelsea din Antonio Conte, yayi gum! Bai furta komai ba dangane da batun. Sai dai rahotanni sun nuna cewa Kocin zai nemi dan wasan gaba har dai Diego Costa ya tashi zuwa Atletico Madrid.

Asali: Legit.ng

Online view pixel