Mutane 9 sun raunana yayinda yan daba suka far ma majalisa

Mutane 9 sun raunana yayinda yan daba suka far ma majalisa

–Yan daban sun kai farmakin ne yayinda yan majalisun na cikin aiki, sun ji ma yan majalisu 5 rauni da kuma ma'aikatan majalisan 4.

–Daga baya wata dakarun sojoji suka kawo agaji inda suka kama yan daba 18 kuma suka mika su ga rundunar yan sandan Ughelli kwamand.

Mutane 9 sun raunana yayinda yan daba suka far ma majalisa
yan daba

Kansiloli da ma'aikatan karamar Hukumar Ughelli ta kudun Jihar Delta sun shiga dimuwa a ranan alhamis 21 ga watan yuli, yayinda wasu yan daba suka kai farmaki majalisan a lokacin wata taro. Mutane 9 suka ji raunuka iri-iri yayinda yan daban da ke rike da makamai irinsu bindigogi, adduna, takubba, da wasu muggan makamai suka far ma duk wanda suka gani.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cew kansiloli 5, ma'aikatan su 3,da magatakatdan majalisan ne suks sha sara daga yan daban. Daga baya wata dakarun sojoji suka kawo agaji inda suka kama yan daba 18 kuma suka mika su ga rundunar yan sandan Ughelli kwamand. Shugaban masu rinjaye , December Saromare, ya tabbatar da faruwan labarin kuma ya kara da cewa yan daban sun tafi da sandar mulkin majalisa Bayan sun fasa tagogin ,sunyi biji biji da kujeru,da sauran su.

Rahoton tace wani babban jami'in yan sanda ya tabbatar da aukuwan hayagagan kuma ya tabbatar da cewan an daure wasu yan daban kuma sun bayyana cewan wani kasugumin dan siyasa da yan majalisun guda 3 ne suka turo su KU KARANTA : An yiwa Bola Tinubu da ‘yarsa Sojan gona a Lagos

“An kwace mota mai launin fari da shude mai lambar JRT 455 XA dasu muggan makamai daga hannun yan daban. Jami'in yan sandan ya fada.

Kwanan nan, wata gungun yan daba sun far ma masu zanga zanga akan koran ma'aikatan da bankuna suka kora a Jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel