Za'a sa wa wani filin jirgi sunan Cristiano Ronaldo

Za'a sa wa wani filin jirgi sunan Cristiano Ronaldo

Nasarar da kasar Portugal ta samu a gasar cin kofin kasashen turai wadda ta gabata a kasar Faransa tare da taimakon shahararren dan wasan kasar Cristiano Ronaldo zai yi sanadiyyar sanya ma filin jirgin da ke tsibirin Madeira wanda kuma yake zaman garin na dan Kwallon sunan sa.

Za'a sa wa wani filin jirgi sunan Cristiano Ronaldo

Jaridar Mirror UK ta ruwaito cewa kawo yanzu dai har ma an yi dan mutum-mutumin shahararren dan wasan na kungiyar Real Madrid a garin nasa tare kuma da sanyawa gidan tarihin garin da otel sunan sa a garin Funchal. Yanzu dai tuni har shire-shire sun kankama don maida ma filin sauka da tashin tsibirin sunan sa watau ‘Madeira Cristiano Ronaldo airport’.

Haka zalika jaridar Mundo Deportivo ma ta ruwaito shugaban karamar hukumar ta su yana tabbatar da cewa yanzu haka dan wasan yana garin nasa yana ci gaba da jinya bayan dawowar sa daga hutun karshen shekarar wasanni a garin Ibiza.

A kwanakin nan dai an ruwaito cewa dan kwallon na Real madrid ya nuna matukar sha'awar sa ta buga wasan su da Sevilla amma kungiyar tasa tace hakan yana da matukar wuya. Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin satin da ya shige ne dan wasan ya halarci taron bude wani katafaren otel din sa a kasar ta Portugal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel