Burin CJTF 250 a Borno ya cika

Burin CJTF 250 a Borno ya cika

Burin matasa 250 ‘yan sojan-sa-kai da ake kira ‘Civilian JTF’ a jihar Borno ya cika, bayan da aka dauki wasunsu aikin soja sakamakon irin gudunmawar da suka ba wa sojoji da sauran jami’an tsaro yaki da ‘yan Boko Haram.

Burin CJTF 250 a Borno ya cika

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ne ya sanar da daukar matasan aikin soja a ranar Juma’a 22 ga watan Yuli a gidan gwamnatin da ke Maiduguri.

Burin CJTF 250 a Borno ya cika

A jawabinsa lokacin ziyararsu ga gwamnan jihar, Bejamin Solomon shugaban sabbin sojojin kuma kwamnadan Fareti ya ce, suna mika godiya ne ga shugaban kasa, da gwamnan jihar, da kuma babban hafsan sojin kasar, a bisa cika musu burinsu na zama cikakkun sojin kasar, sannan ya yi fatan cewa za’a ba sauran matasa damar bautawa kasar su a sauran hukumomin jami’an tsaro.

Sabbin matasan sun kasance suna taimakawa sojojin Najeriya ne a yakin da suke yi da ‘yan Boko Haram Bayan da suka dauki makamai suka shiga gaba wajen kare da jihar da kuma karfinsu da kuma lokacinsu na ganin bayan ‘yan ta’addan

Idan za’a iya tunawa, matasan sojan-sa-kai sun taimaka matuka wajen samar da zaman lafiya da kuma tsaro a yankunan da ke hannun ‘yan ta’addan Boko Haram, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamaw,  inda sojoji da ‘yan Yanda ba su da tasiri.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel