Kungiyar Liverpool Zata Saye Dan wasa Na 6 A Kakar Bana. 

Kungiyar Liverpool Zata Saye Dan wasa Na 6 A Kakar Bana. 

 -Liverpool Suna Shirye Da Sayen Dan Wasar Newcastle George Wijnadun.     

 -Dan Wasan Na Tsakiya Ze Zama Da Wasa Na 6 Da Kungiyar Ta Saya Kakar Wasar Bana.  

Kungiyar Liverpool Zata Saye Dan wasa Na 6 A Kakar Bana. 
    

Liverpool suna shirye da sayen dan wasan Newcastle Georgino Wijnaldum bayan sun gama yarjejeniyar £25 daa kungiyar kamar yadda Liverpool suka ce, dan kasar Holland ze tafi gurin gwajin lafiya ranar Juma'a a garin Liverpool,an tattaro mana bayanai cewa dan wasan ze hadu da Jurgen Klopp da sauran yan wasar kungiyar in komai ya tafi dai-dai,munji cewa an saya dan wasan kimanin £23m da doriyar £2m.

Dan shekara 25 ya jefa kwallo 11 a gasar premier league kakar wasar bara,saboda fadawaa gurbin gajiyayyu da kungiyar tayi yasa shi jin barin kungiyar Newcastle.Ze zama dan wasa na 6 da kungiyar zasu saya,kuma shine dan wasa mabiyin wanda yafi kowa tsada a kungiyar bayan sayen Mane £30m daga kungiyar Southamptom. Liverpool da sun riga sun sayi Mane,Joel Matip,Marko Grujic,Loris Karius da Ragnar Klavan kuma ana tsammanin sayen Wijnaldu da wasu ma da yawa.

KU KARANTA : Idan dama ta kiya zan koma hagu inji Mourinho

Duk da ya rasa samun sayen dan wasan tsohuwar kungiyar shi Durtmund take zawarci Mario Gotze,amma har yanzu yana fatar sayen Piotr Zielinski daga udinese da Mahmoud Dahoud daga Monchenladbach.

Asali: Legit.ng

Online view pixel