Real Madrid ta sake kin amincewa da tayin Man utd

Real Madrid ta sake kin amincewa da tayin Man utd

Kungiyar kwallon kafa ta Real madrid ta sake kin amincewa da tayin Man utd na siyen dan wasan ta na baya Raphael Varane.

Real Madrid ta sake kin amincewa da tayin Man utd

Shi dai Varane din yana ci gaba da shan wahala wajen samun wurin buga wasa na din-din-din a kungiyar ta sa ganin yadda mai horar da su Zinedine Zidane ya fi aminta da ya sanya Ramos da Pepe a tsakiyar. Kwazon da Pepe ya nuna a gasar da ta gabata ma dai ta cin kofin kasashen turai na nuni da cewa Pepe zai ci gaba da buga wasa har zuwa nan gaba a Real din.

Duk da sanin tabbacin wurin buga wasa na din-din-din da Varane din zai samu a kungiyar Man utd dan wasan ya amince ya ci gaba da zama a kungiyar sa ta Real yana mai fatan zai gaje Pepe wanda yanzu haka yake da shekaru 33. Yanzu dai Mourinho ya mai da hankalin sa kacokan kan sabon dan wasan da siyo Eric Bailly a matsayin dan wasan bayan sa. A wasu lokuta da dama ma dai Mourinhon yana kamanta Bailly din da Varane.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel