Lola Alao Rodiat ta bayyana dalilin da ya sa ta musulunta

Lola Alao Rodiat ta bayyana dalilin da ya sa ta musulunta

-Yar wasan kwaikwayon Nollywood Lola Ajao wacce ta musulunta kwannan nan ta fadi dalilanta na aikata haka

-Yar wasan ta kuma chanja sabon suna

-Ta shiga layin su Lizzy Anjorin, Fathia Balogun da sauransu

Lola Alao Rodiat ta bayyana dalilin da ya sa ta musulunta
Lola Alao
Lola Alao Rodiat ta bayyana dalilin da ya sa ta musulunta
Lola Alao

Sananiyar yar wasan kwaikwayon Nollywood Lola Alao ta yasar da tsohon addininta na Kirista zuwa addinin Musulunci.

Kyayyawan yar wasan ta tabbatar da shiganta addinin musulunci. Ta yi sanarwan ta shafinta na sadarwa bayan labarin ya bazu. Ta rubuta:

“Assalamu alaikum, zuwa ga dukkan masoyyana da abokai na, Allah ya biya maku dukkan bukatun dake zuciyarku, ina dai son kowa ya san cewa an haifeni a gidan Musulmai, sunan marigayin mahaifina Lasisi Alao, don haka na koma kan tafarkin sasallata ta hanayar Alhaji Yusuf Adepoju (Acadip). Allah ya albarkace shi da kuma dukkan abokanan arziki da masoyyana……….. Nagode ina kaunarku dukka.. Rohdiat Omolola Alao Ajibola.

Yar wasan kwaikwayon ta musulta a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, a Academy of Islamic Propagation, Nigeria (ACADIP). Yar wasan ta kuma samu sabon suna Rhodiat.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar OPC sun gargadi mayakan Niger Delta

A yan kwanaki da suka shige, munji cewa nan da sannu rikicin addini mai tsanani na iya afkuwa a kasar Najeriya idan ba’a mayar da hankali ga rahotanni da yan leken asirin al’umman Najeriya ke kawo ba. A cewar wata majiya da jaridar Sahara Reporters ta samo, an motsa rikicin ne a siyasance, domin girgiza hadin kan kasa, ta hanyar farfado da kisan kiristoci da musulmai sukayi a arewa kwanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel