Yan wasa 10 da ka iya zama zakaran UEFA 2015/16

Yan wasa 10 da ka iya zama zakaran UEFA 2015/16

 

– UEFA ta fitar da sunayen mutane 10 da za su iya cin kyautar zakaran dan wasan Turai.

– Akwai yan wasa 3 ‘yan asalin Kasar Jamus da kuma 2 daga Kasar Portugal.

– UEFA ta cire wasu ‘yan wasa 3 da ba ayi tsammani ba.

Yan wasa 10 da ka iya zama zakaran UEFA 2015/16

 

 

 

 

 

Hukumar Kwallon Kafar Nahiyar Turai, UEFA ta fitar da jerin sunayen yan wasa 10, wanda a cikin su ne za a samu wanda zai lashe kyautar zakaran dan wasa na Nahiyar ta Turai na shekarar 2015/16. Daga baya za a rage sunayen yan wasan daga 10 zuwa 3, wanda daga nan za a zabi zakara cikin su. Ga sunayen ‘yan wasan su 10 da ke neman kyautar:

Dan wasan na Kasar Wales ya taka rawar gani, inda ya jagoranci Kasar sa a Gasar UEFA EURO 2016 har suka kai wasa na kusa da karshe, sai dai Portugal ta taka masu birki da ci 2-0. Bale ya ci ma Real Madrid kwallaye 19 a shekarar har suka dauki kofin ‘UEFA Champions League’.

Tsohon Golan mai shekaru 38 ya taimaki Juventus wajen ci kofin Seria A na Italy karo na 3 (A jere). Tarihi ya tabbatar da cewa babu dan wasan da ya buga ma Kasar Italiya kwallo kamar sa.

Shi ne dan wasan da ya fi kowa kwallaye a Gasar UEFA EURO 2016, shi aka ba lambar ‘gwal’. Ya ci ma Atletico Madrid kusan kwallaye 30 a shekarar, ya kai su har wasan Karshe na ‘UEFA Champions league’.

Kroos ne tsakiyar Kasar Jamus. Ya rikita kowa a Gasar UEFA EURO 2016 da aka buga. Kroos da Modric ne a tsakiyar Madrid, inda suka kai Kungiyar zuwa wata nasara a gasar ta UEFA Champions league.

Dan kwallon duniyan ya ci kwallaye 41 a bara. Barcelona ta samu cin kofin La liga da kuma Copa del rey. Ya kuma jefa kwallaye 5 a Gasar COPA AMERICA duk da an ci su a wasan Karshe.

Mueller ya ci wa Bayern Munchen kwallaye kusan 20 a Gasar gida, BundesLiga. Sai dai dan wasan bai yi abin kirki ba UEFA EURO 2016 wannan karo.

Golan duniya kenan, Manuel Neuer. Ya taimaki kasa da kulob din sa a raga wannan shekarar.

Wanda ya fitini kowa kenan a Gasar UEFA EURO 2016. Yana cikin wadanda suka sa Kasar Portugal ta dauki kofin EURO 2016. Ya kuma dauki UEFA Champions league da Real Madrid.

CR7 kenan! Ana tunanin shi ne zai dauki wannan kyauta. Ya jagoranci Kasar zuwa wasan Karshe a UEFA EURO 2016. Kuma ya ci kwallaye 16 a Gasar UEFA Champions league kadai, wanda Real Madrid din ta yi nasara. Ya kuma zo na biyu a La liga da kwallaye 51 cikin wasanni 48.

Shi yazo na daya wajen cin kwallaye a Kasar Spain, ya buge CR7, bayan da ya ci kwallaye 40 cikin wasa 35 kacal. Yana dai da kwallaye 59 wannan shekarar.

KU KARANTA: ZA A HARAMTA KASAR RUSSIA ZUWA GASAR OLYMPICS

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel