Abdulmumin Jibrin ya fasa kwai

Abdulmumin Jibrin ya fasa kwai

–Labarai iri-iri na fitowa akan almundahana da babakeren da ke faruwa a majalisan wakilan tarayya ,yayinda Abdulmumin jibrin , tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi da aka cire jiya ya fasa kwai.

–A cikin asiran da ya tona, dan majalisan ya tuhumci kakakin majalisan,Yakubu Dogara, da yunkurin canje-canje a cikin kasafin kudin kasa ta shekarar 2016

–Yace shi ne da kansa ya yanke shawaran barin kujeran shugaban kwamitin kasafin kudi ,ba Koran shi akayi ba kamar yadda ake fada

Abdulmumin Jibrin ya fasa kwai

Kwana daya kacal bayan ya sauka daga karagan shugabancin kwamitin kasafin kudi,Abdulmumin Jibrin ,yayi wasu maganganu akan kakakin majalisa,Yakubu Dogara da wasu shugabbanin majalisar wakilai ta kasa.

Ya tuhumci kakakin majalisan da wasu shugabannin majalisar da rashawa da almundana ,kana da yunkurin canje –canje cikin kasafin kudin kasa ta shekarar 2016.

Jibrin,wanda ya nanata cewa muraus yayi,ba koransa akayi ba kamar yadda ake fada, yace shugabannin majalisan wakilai wanda ya kunshi  yakubu dogara,mataimakin sa ,yusuf lasun, cif wip, alhassan doguwa, da shugaban marasa rinjaye ,leo ogor, sun razana da ayyukan san a rashin hada kai da su a matsayinshi na shugaban kwamitin.

KU KARANTA : EFCC ta kama tsohon mataimakin kakakin majalisa

Yayi maganganu iri-iri ta shafin sadr da zumuntarsa ta twita da yammacin yau ,alhamis,21 ga want yuli,2016. Yace:

 “Ya zama mini wajibi in fito inyi Magana bayan saurarn jawabin kakakin majalisa yakubu dogara akan dalilin da yasa nayi murabus da kujera na a matsayin shugaban kwamitin kasafin kudi. Ko shakka babu,ni na fada ma kakakin cewa ina son in bar kujeran.

“Amma maganan yakubu dogara gaba dayan ta kage ne,karya ne,zalunci ne. Wadannan shugabannin majalisan dama hankalin su bai kwanta da kasancewana mai mababbancin ra’ayi ba  da kuma rashin amincewan da nayi na yunkurin su baiwa kansu kudi N40biliyan daga cikin N100bilyan din da aka ba majalisar dokoki gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel