Mai Question Mark Music Kevin Lucciano Ya Shiga Siyasa

Mai Question Mark Music Kevin Lucciano Ya Shiga Siyasa

  -Yana Takarar Shugaban Karamar Hukumar Apapa Karkashin Jam'iyar APC.                 

Sanannen mai gidan waka na Najeriya Lucciano (COE) na Question Mark Entertainment wanda ya fito da yawancin mawaka a Najeriya ya nuna kudurinshi na takarar neman wani matsayi. Lucciano ya shiga Jam'iyar APC da katin da yake nuna dan jam'iyar ne,yana bukatar neman takarar shugaban karamar Apapa zabe mai zuwa a Jihar Lagos.

Mai Question Mark Music Kevin Lucciano Ya Shiga Siyasa
Kevin Lucciano

Question Mark ya fito da jarumai a kungiyar mawakan Najeriya wanda ya hada da Asa,Harry Song,Ego da Sauransu. Lucciano ya dade da muradin shiga siyasa,Ranar asabar Afrilu 27 aka zabe shi a matsayin shugaban rikon kwarya na (PMAN) na kasa bayan abakan hamayyar shi Gospel Artist,Showbiz Promoter da Skid Ikemefuna sun jaye mashi.

KU KARANTA : Ameachi da sauransu sun biya milliyan 100 don shiga APC?

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel