Gasar yan makarantar Najeriya na iya kwalliya dasa Kaya

Gasar yan makarantar Najeriya na iya kwalliya dasa Kaya

An bayyana ranar 12 da 13 ga watan Agustan shekaran 2016 za'a gudanar da gasar iya kwalliya da kuma iyasa Kaya nayan makarantan Najeriya karo na hudu.

Wasan daya daukaka matasa akalla 150 a harkan wa'anda sukayi suna kuma suka samu ci gaba a masana'antar kwalliya da iya sa Kaya na najeriya. Bankin wema plc ke daukan nauyin wasan, wacca tana daga cikin sanannun bankunan kasar nan, dakuma. Myhair limited.

Shidai wannan gasar mai taken [NSFDW], Black bold fashion house ne suka fara assasashi tare da hadin gyuwan Africa fashion week London da kuma furodusan dake kula da harkan kwalliya da iyasa Kaya na duniya, wato Mahogany production, tare da tare da furadusoshi kwalliya da iyasa kaya na Afirica dake landan tare da shashin su na najeriya.

KU KARANTA : Blessing Okagbare taci gasar tseren mita 100

Dalilin kirkiro da NSFDW saboda a baiwa yara yan makaranta masu basira daman nuna kwarewar su a harkan, wanda zai taimaka masu su zama manyan gobe. Wa'anda sukaci gasar zasu sami gudun mawar daukan nauyi na shekara daya daga AFWN da kuma kaya masu kyau daga kamfanin PR, kuma zasu samu sabon na'uran dinki na komfuta na zamani daga kamfanin Zinsu tech Nig plc, tare da kuma daukan nauyi na kudi daga bankin wema Nig plc, inda na daya dana biyu zasu samu kyaututuka daga kamfanonin Tolumi fashion people limited, Zunsu tech Nig limited dakuma Xtlen ta shoppe.  Kudin shiga kallo na yan makaranta naira dari biyar, wa'anda ba yan makaranta ba kuma dubu daya, sai kuma wajan zama na musamman naira dubu biyar.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel