An fitar da tsarin bikin bizne Stephen Keshi

An fitar da tsarin bikin bizne Stephen Keshi

An kammala shirye-shire da kuma tsare-tsaren shagulgulan bizne tsohon mai horarwar Super Eagels Stephen Keshi. Kwamisjina yada labarai wanda kuma memba din kwamitin shire-shiren biznewar Patrick Ukah ne ya bayyana haka ga manema labarai.

An fitar da tsarin bikin bizne Stephen Keshi
Late Stephen keshi

An dai tsara shagulgulan ne daga ranar Alhamis 28 ga watan Yuli zuwa Lahadi 31 da watan na wannan shekarar ta 2016. Ukah din ya bayyana hakan ne jiya laraba 20 ga watan Yuli a garin Asaba. Ya ce za'a fara shagalin ne a cocin katolika dake garin Benin a ranar Alhamis din.

Ya kuma kara da cewa akwai wasan kwallo da za'ayi a ranar da marece duk dai a garin na Benin. A cewar sa, ranar ne kuma za'a tafi da gawar tasa zuwa Asaba. Acan din ma dai za'a cigaba da shagulgulan ne a wata cocin ta katolika har zuwa dare.

Ranar juma'a kuma sai a tafi da gwar zuwa kauyen Illah yayin kuma da za'a dan tsaya fadar sarkin garin. Za'a kammalla bukukuwan bizne Keshin dai a ranar Lahadi a garin nasu na Illah.

Source: Legit

Online view pixel