Shin Saraki ya koma PDP kuwa?

Shin Saraki ya koma PDP kuwa?

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Senata Bukola Saraki ya fitar da sanarwa inda yake fayyace matsayarsa game da zantukan dake yawo na cewar ko ya koma jam'iyyar sa ta da watau PDP.

Shin Saraki ya koma PDP kuwa?
Saraki 

Shi dai Saraki yayi gwamnan jihar Kwara na tsawon shekaru 8 kafin daga bisani ya tafi majalisar dattijan inda kuma ya canza sheka zuwa APC a gabanin zabukan 2015. Bayan zabukan ne dai ya fara samun matsala da sabuwar jam'iyyar tasa ta APC bayan da ya lashe kujerar shugaban majalisar dattijai a wani salo wanda ya bakantawa jam'iyyar tasa ta APC rai.

Sai dai tun bayan faruwar hakan ne yak ci gaba da fuskantar matsi da jam'iyyar tasa tare kuma da zarge-zargen sa da akeyi a gaban kotu. Wannan ne ma yasa ake ta rade-raden cewa ko ya koma tsohuwar jam'iyyar tasa. Harma dai wasu kafafen yada labarai da dama (amma banda Legit.ng) suka fara ruwaito cewar Sarakin ya je ya gana da tsohon shugaban kasa Jonathan jiya laraba 20 ga watan yuli a wani yunkuri da ake ganin yana zaman share fage ne gareshi ta yadda zai iya komawa jam'iyyar tasa nan gaba.

Sai dai kuma daga baya mai magana da yawun Saraki din Bamikole Omishore ya musanta zancen inda ya sake jadda cewa shugaban majalisar yana nan daram a jam'iyyar APC.

Ga dai sanarwar da fitar din nan a kasa.

"An jawo hankalin shugaban majalisar dattijai tare da mukarraban sa da cewa rahotanni na ta yawo ana cewa ya koma jam'iyyar PDP to tabbas ba hakan bane. Zancen karyace kawai don kuwa Bukola Saraki yana nan APC daram dam."

"A matsayin sa na shugaban majalisar dokokin kasar nan hakan ne ya bashi hurumin zuwa taron jigogin jam'iyyar pDP da aka gayyace shi a jiya. Da yaje kuma ya shafe kimanin mintuna 30 kafin daga bisani ya tafi".

"Daga karshe shugaban majalisar dattijan yana kara jaddama dukkan magoya bayan sa da ma yan Najeriya baki daya cewa yana nan jam'iyyar sa ta APC".

Asali: Legit.ng

Online view pixel