Sanata ya soki ‘Auren Hisbah’ na gwamnatin Kano

Sanata ya soki ‘Auren Hisbah’ na gwamnatin Kano

-Wani Sanata ya soki auren zaurawa da ‘yan mata da gwamnatin Kano ke yi

-‘Yan Najeriya na bukatar ayyuka ne ba matan auren ba, a cewarsa

-Wasu na tambaya ko me yasa Sanatan bai ce komai ba game da gidajen sayar da jarirai a kudu?

Sanata ya soki ‘Auren Hisbah’ na gwamnatin Kano
Sanata Ben Murray -Bruce ya kalubanci gwamnatin Kano kan auren mata da zaurawa da ta ke yi.

Sanata Ben Murray-Bruce dan kasuwa kuma mai kamfanin Silver Bird mai shirya gasar sarauniyar kyau, ya bayyana ra’ayinsa kan aurar da mata zaurawa da hukumar Hisbah za ta yi a jihar Kano.

A wani sako da Sanatan ya lika a shafinsa na muhawara da sada zumunta na Facebook, dan kasuwar ya soki shirin gwamnatin jihar Kano na aurar da matan ne da hukumar Hisbah ta jihar ke yi, a inda ya ke cewa, kamata ya yi ta mayar a hankali wajen samar da ayyukan yi a maimakon aurar da matan. Ya kuma kara da cewa hankan wani abin takaici ne.

Sai dai wannan ra’ayi na dan majalisar ya janyo martani daga wasu ‘yan Najeriya a inda wasu ke ganin  bekan sa, ganin cewa shi ne shugaban shirya bikin gasar sarauniyar kyau mai janyo tir daga addinan Islama da na Krista, wasu kuma na tambaya ina me yasa bai ce komai ba kan gidajen da aka bankado da ake yiwa ‘yan mata ciki ana sayar da jariransu a kudancin kasar.

Gwamnatin jihar Kano na shirin aurar da mata 10,000 wadanda suka hada da zaurawa da ‘yan mata da kuma wadanda mazajensu suka mutu, a wani biki da gwamnatin saba yi duk shekara tare da hukumar Hisbah.

‘Yan Najeriya dai na cigaba da fadin albarkacin bakinsu, ko menene naka?

Asali: Legit.ng

Online view pixel