Ogbeh yayi magana dangane halin da ‘Yan Najeriya ke ciki

Ogbeh yayi magana dangane halin da ‘Yan Najeriya ke ciki

 

 – Cif Audu Ogbeh ya nuna takaici game da halin da ‘Yan Najeriya ke ciki.

– Ministan gonan Najeriya yace mutanen Kasa na fama da yunwa.

– Minista Audu Ogbeh yace Gwamnatin APC na kokarin shawo kan matsalolin da ake fuskanta.

Ogbeh yayi magana dangane halin da ‘Yan Najeriya ke ciki

 

 

 

 

 

Cif Audu Ogbeh wanda shine Ministan gona na Najeriya ya furta cewa ana fama a yunwa a cikin Najeriya. Ya furta wannan magana ne a ranar Laraba, 20 ga Watan Yulin Najeriya. Minista Audu Ogbeh ya yarda cewa akwai karancin abinci a cikin Kasa. A taron Majalisar zartarwar Kasar (FEC) Ministan yake bayyana cewa mutanen Najeriya na cikin wani mawuyacin hali, na masifar yunwa. Bayan taron ne Ministan ya gana da ‘yan Jarida inda yayi wannan magana. Shugaba Buhari ne dai ya shugabanci taron da aka gabatar a ranar Jiya Laraba, 20 Ga watan Yuli 2016 a fadar Shugaban Kasa na ‘Villa’ a Garin Abuja. Haka ma dai Ministan al’amurran mata Aisha Alhassan ta zanta da ‘yan Jaridun, da Kuma Mista Femi Adesina yana cikin wadanda suka tattauna da manema labaran. Ministan na Najeriya, Ogbeh yana cewa dai duk da haka Kasar Najeriya akwai sauki idan aka kamanta da Kasar Venezuela, inda babu abincin da mutanen Kasar za su ci. Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Buhari ta APC na iyaka bakin gwargwadon magance wannan matsala.

KU KARANTA: SUNAYEN DA ‘YAN NAJERIYA SUKA LAKA WA SHUGABA BUHARI

Ministan noma na Najeriya ya bayyana irin halin da ‘yan Kasa ke fama na yunwa, ya kuma yi alkawarin kawo karshen wannan rikici cikin nan da Shekara daya da rabi. Ministan yana tabbatar da cewa Kasar za ta samu isasshen hatsi; Shinkafa, wake da sauran su zuwa wannan lokacin. Gwmanati ta kawo wani tsari da sa ma suna ‘The Green Alternative’ domin ganin karshen wannan matsala. Yace Gwamnati ba za ta huta ba har sai an kawo karshen wannan matsala.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel