Kisan basarake a Plateau a bi a hankali –Sarkin Musulmi

Kisan basarake a Plateau a bi a hankali –Sarkin Musulmi

-Kisan basaraken gargajiya a Plato ya janyo Allah wadai

-Ana zargin Fulani makiyaya da yin kisan

-Sarkin Musulmi ya ce a bi a hankali

Kisan basarake a Plateau a bi a hankali –Sarkin Musulmi
Mai alfarama Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar, REUTERS/Afolabi Sotunde (NIGERIA) - RTR1N1ZM

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya ce kar a yi riga malam masallachi dangane zargin kisan wani basaraken gargajiya a jihar Plato.

KU KARANTA: Tarihi: Sarkin Musulmi na farko a Lagos 1895

Sarkin Muslmin ya fadi hakan ne ziyarar da ya kai fadar Gwom gom Jos a ranar Laraba, a inda ya jajantawa al’umar jihar dangane da kisan sannan ya yi kira ga ‘yan jaridu da su daina yada jita-jitar cewa Fulani ne suka yi kisan ba tare da jiran sakamakon binciken jami’an tsaro ba.

Sarkin musulmi ya kuma ce, “Ya kamata mutane su daina daukar doka a hannunsu, ya kuma  kamata a rika tona asirin bata gari a al’umma….”

KU KARANTA: An hallaka wani mai tsire a bakin tukubarsa a Calabar

A ranar Litinin 18 ga Yuli ne aka hallaka Saf Ron Kulere, Cif Lazarus Agai a kan hanyarsa ta dawowa daga gona tare da matarsa da dansa da kuma wani dansanda mai tsaron lafiyarsa, yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude musu wuta a inda suka hallaka su.

Washe gari bayan kai harin ne, wasu gungun matasa suka tsare hanyoyin yankin tare da kona gidajen jam’a bayan da suka dora alhakkin kisan akan Fulani makiyaya da ke zaune a yankin. Suna masu zargin cewa an kashe basarake ne saboda rashin amincewa da shirin gwamnati na samar da wurin kiwo a yankin.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel