An kara ma yan sanda 22 girma zuwa AIG

An kara ma yan sanda 22 girma zuwa AIG

– Hukumar ayyukan yan sanda PSC ta amince da karawa kwamishanoni 22 girma zuwa matsayin AIG

– Ta amince da karawa 29 zuwa matsayin Kwamishana

Hukumar ayyukan yan sanda ta amince da kara girman kwamishanoni 22 zuwa matsayin AIG

An kara ma yan sanda 22 girma zuwa AIG
sifeton yan sanda Ibrahim Idris

Wannan ta kunsu ne a wata jawabin da shugaban yada labarum hukumar,Ikechukwu Ani, a Abuja ranar laraba 20 ga watan yuli. Ani yace an kara ma yan sanda girma ne saboda gabatar da su da akayi kuma sabode maye gurbin da aka bari na matsayin AIG da kwaminshana.

Anyi binciken kwamishanonin karkashin shugabancin shugaban hukumar ,mike okiro,da kuma wasu mambobin hukumar.

Kakakin hukumar yace hukumar ta duba kamatan samun girma

“Yawancin sabbin AIG din an tura su zanal kwamand kuma sauran 9 an tura su kwamishanonin kwamand. Yace

KU KARANTA : Matar Tinubu ta rubuta takardar koke zuwa ga IGP

Sabbin Karin girman sun zo ne kwamanki kadan bayan hukumar ta amince da Karin girman sabbin AIG 18 da kwamishanoni 37. Hukumar ta tabbatar da tura AIG 4, yayinda cikin sabbin kwamishanonin, 12 za su kasance masu kula da kwamand 12, kuma 10 zasu zama shugabannin tawaga irin ayyuka,horo,makarantan yan sanda, fasaha,kasuwanci da sauran su.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel