Shugabancin Kasa : Yan Najeriya sun ki Atiku.   

Shugabancin Kasa : Yan Najeriya sun ki Atiku.   

Rahoton cewa" Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Aabubakar yana kokarin takara shugabancin kasar nan a karkashin jam'iyar APC ya hadu d rashin amincewar wasu yan Najeriya. Atiku wanda aka rohoto cewa yaa dade yana rainon kudurinshi na zama shugaban kasa,ya nuna bukatarshi lokacin da ya ziyarci shugaban jam'iyar APC Cif Odigie-Oyegun a sakatariya jam'iyar dake Abuja ranar talata 19,Juli.

Shugabancin Kasa : Yan Najeriya sun ki Atiku.   

Kamar yadda muka ji, Atikun ya ziyarci sakatariyar dan sanar da kanshi da shuwagaban nin jama'iyar akan zaben fidda gwani da jam'iyar zasu yi shekara 2019,amma tunda labarin kudurin Atiku ya fita na kudurin takarar shugaban cin kasar,waasu yan Najeriya sun fara nuna adawarsu akan takarar tsohon mataimakin shugaban kasar kan rashin gaskiya.

Wasu sun bayyana Atiku a matsayin dan siyasar ta leko ta koma sun bukata a saka matashi wanda zeyi abin a zo a gani.  Rahoton rade-raden dawowar Nuhu Ribadu APC yana so ya kawo ma Atiku cikas kan takararshi. Ribadu tsohon shugaban EFCC kuma tsohon dan takarar shugaban kasa jam'iyar CAN kafin su hade da APC.

KU KARANTA : Atiku Abubakar yayi korafi kan komawar Ribadu APC

Tsohon shugaban na EFCC da tsohon dan takara Gwamna Adamawa Marcus Gunduri an rohoto sun karbi takarda daga jam'iyar APC yankin Adamawa na yarde masu su dawo jam'iyar APC tare da magoya bayansu.Jaridar Nation tace sakamakon wannan cigaban, Atiku da Gwamna Bindo da wasu mutane 2 sun nuna rashin amincewarsu ga shugaban jam'iyar APC Cif Odigie-Oyegun da (NWC) akan dawowar Ribadu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel