Yan sanda sun kama wani Fasto kan tsagerun Neja Delta

Yan sanda sun kama wani Fasto kan tsagerun Neja Delta

  -Yan sanda suna tuhumar wani Fasto a garin Warri kan zarginshi na daukar nauyin tsagerarrun Neja Delta.             

 -Ana Kuma Zargin Mutumin da boye makamai a coci da Gidansa.

Yan sanda sun kama wani Fasto kan tsagerun Neja Delta
tsagerun neja deta

Wani Bishop a Cocin New Generation a garin Warri Yan sandar jahar Delta sun kama shi kan rohoton da aka kawo masu na daukar nauyin kungiyar tsagerun Neja Delta (NDA). Jaridar punch ta rohoto cewa Bishop din da ba'a fada sunanshi ba,wanda ya fito daga garin Ogbiri ta Egbema masarautar Ijaw a garin Warri wanda ke shugabancin cocin New Salvation Zion Church of christ a Igbodo.

Yan sanda sun bayyana ma manema labarai  an gayyaci Bishop din cocin bayan takardu 2 naa korafi da aka aika na cewa yana daukar nauyin tsagerun.Anyi binciken a babban ofishin yan sandan Warri na jahar Delta, an tsare Bishop din daga kare 8 na safe zuwa 8 na yamma a makon da ya gabata 13,Juli kafin a bashi damar tafiya da bashi umarnin dawowa da safe.

KU KARANTA : Yadda gurbatar muhalli ke shafar Neja Delta

A takardar zargin an zayyana cewa Bishop din yana boye makamai a gida da coci,yan sanda sun binciki gidan Bishop dke Bendel Estate a Effurun da cocin shi dake Igbodu a garin Warri,amma ba'a samu komai a gidan Bishop din ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel