An-yanka-ta-tashi: Hukumar EFCC ta gayyaci wani dan majalisar wakillan Najeriya

An-yanka-ta-tashi: Hukumar EFCC ta gayyaci wani dan majalisar wakillan Najeriya

Hukumar hana cin hanci da rashawa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta kama wani dan majalisar wakillai mai suna Nse Bassey Ekpenyong mai wakiltar mazabar Oron dake jihar Akwa ibom a kudancin Najeriya bisa zarginsa da gabatar da takardun boge.

EFCC ta kama wani dan majalisar wakillai

Wata kungiya wadda bata gwamnati ba dai ce ta kai karar dan majalisar ga hukumar EFCC din tana zargin sa da damfara kamar dai yadda gidan jaridar Sahara reporters ya ruwaito. Kungiyar wadda ba ta gwamnati ba dai tana zarginsa ne da gabatar da takardar shaidai kammala difloma daga makarantar dake jihar Abia ga hukumar zabe mai zaman kanta a lokacin zabukan da suka gabata na 2015.

Haka zalika kungiyar tana zarginsa da amsar haramtattun kudaden albashi da ma sauran alawus-alawus tun daga lokacin da ya zamo dan majalisa. Binciken da hukumar EFCC din ta gudanar dai ya tabbatar da cewa dan Majalisa Ekpenyong din dai bai halarci makarantar da ya zayyana ba haka kuma takardar da dan majalisar ya gabatar itama ba daga makarantar take ba.

Kawo yanzu dai yan bada belin dan majalisar yayin da kuma hukumar ta EFCC tace tana cigaba da bincike.

A wani labari mai kama da wannan kuma shugaban hukumar INEC na garin Abia ma ya sha tambayoyi a gurin hukumar EFCC din bisa zargin sa da hannu cikin wasu kudade da suka kai N23bn da aka rarraba gabanin zaben 2015.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel