Atiku Abubakar yayi korafi kan komawar Ribadu APC

Atiku Abubakar yayi korafi kan komawar Ribadu APC

-Neman zaben shugabanci kasar Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a karkashin jam’iyyar APC ya kuma samun barazana kuma an rahoto cewa yayi zanga-zanga kan wannan

-Anyi imani Sansanin siyasar sa bata daidaita ba inda akayi duba da yanda ake rokon shugaban wata kungiyar adawa, da Nuhu Ribadu su dawo Jam’iyyar APC

-Yunkurin da Atiku Abubakar da masu mara masa baya ke yi don chanja tsarin bai samu karbuwa ba, yayin da aka rahoto cewa babban hedkwata jam’iyyar APC ta kasa da shugaban kasa sun goyi bayan daowar Ribadu

Atiku Abubakar yayi korafi kan komawar Ribadu APC
Nuhu Ribadu,

An rahoto cewa yunkurin dawowar Nuhu Ribadu jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya sa sansanin siyasar Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, cikin rashin tabbas, da kuma rashin magama cikin neman shugabancin kasa.

Ribadu, tsohon shugaban hukumar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), ya kasance dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) kafin jam’iyyar ta hade da jam’iyyar APC.

An rahoto cewa Nuhu Ribadu ya amince da dawowa jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban kasa Jonathan ya kafa wani muhimmin aiki

Ribadu ya bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda a karkashinta ne ya tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa, amma ya fadi a zangon farko.

An samo rahotannin cewa tsohon shugaban hukumar EFCC, da wani dan takarar gwamna, Marcus Gundiri, sun samu wasika daga jam’iyyar APC sashin Adamawa kan cewa zasu basu goyan baya idan suka dawo Jam’iyyar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa bisa ga wannan ci gaban, Atiku Abubakar, Gwamnan jihar Adamawa Jibrilla Bindow, da wasu mutane biyu sunyi zanga-zanga ga shugaban jam’iyyar ta kasa, John Odigie-Oyegun, da kuma kungiyar National Working Committee (NWC) na jam’iyyar kan dawowar Ribadu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel