An haifi jariri da yatsu 31 a kasar Sin.

An haifi jariri da yatsu 31 a kasar Sin.

Abubuwan ban mamaki basa karewa a duniya, a haka ne aka samu wani jariri da aka haifa a kasar Sin mai yatsu 31 a hannaye da kafafuwar sa.

An haifi jariri da yatsu 31 a kasar Sin.
Jaririn mai yatsu 31

Mahaifiyar jaririn ta samu kulawa mai kyau a lokacin da take dauke da cikin nasa, an dauki hotunan cikin nata da dama, amma ba’a gano cewa zata hafi irin wannan jaririn ba, jaririn na nan cikin koshin lafiya.

Yatsu 15 ne a hannayensa, da kuma 16 a kafafunsa. Bugu da kari, tafuka biyu jaririn ke dasu a duk tafin hannunsa, amma babu babban yatsa a tare dasu. Iyayen jaririn sun yi kokarin neman a cire ma yaron yatsun ta hanyar tiyata, amma fa akwai tsada, kuma akwai hatsari.A yanzu haka watanni kadan yaron ya kwashe a duniya.

An haifi jariri da yatsu 31 a kasar Sin.
An haifi jariri da yatsu 31 a kasar Sin.

Ana kiran wannan matsala da suna ‘polydactyl’ wato matsalar samun gabbai dayawa, sa’annan ba wani sabon matsala bane sosai, a duk cikin mutane 1000 ana samun mutum daya wanda ke zuwa da sama da yadda aka saba.

An haifi jariri da yatsu 31 a kasar Sin.

Kamar yadda kake gani, uwar yaron ma na da irin wadannan yatsu, sa’annan tana da wani yatsan da yaki girma. Amma bincike ya nuna ba kasafai ake samun yatsu 31 ba.

Sai dai iyayen wannan jaririn talakawa ne, kuma iyayensa na yin bakin kokarinsu don samun isashshen kudin da zai isa ayi mai aikin tiyata kafin jaririn ya cika shekara daya, wanda hakan zai sa ayi aikin cin sauki saboda kafin kashinsa yayi kwari. Muna fatan jama’a zasu tallafa ma iyayen jaririn nan don a ceto rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel