Fasto ya bulale mamban Cocin sa.

Fasto ya bulale mamban Cocin sa.

Fasto Bolaji Idowu na cocin Harvesters International Christian center (HICC),a ranan litinin ,18 ga watan yuli , yayi wani abun ban mamaki kuma ban dariya a wata huduban da ya bayar mai take "Ubangiji na fushi da ni ne?".

Abin tamkar wasan kwaykwayo faston ya dauko tsimagiya domin ladabtar da wani mamban da ya fito a matsayin wanda ya ma Ubangiji laifi,kawai sai wani ya fito zai dauke bulalan da ya kamata wanda yayi laifin ya sha domin ya aikata ma Ubangiji zunubi.

Fasto ya bulale mamban Cocin sa.

Bayan wasan kwaykwayon, Faston ya nuna cewa yaron da yayi laifin ya samu gafara tunda wani ya dauke mai,saboda haka ba sai ya ci bulala ba.

Faston ya fada cikin hudubanshi da ke magana akan wayar da kansu da kuma bude musu ido kan cewa Ubangiji bazai yi fushi da su ba, yayi bayanin cewa tunda sunyi imani da yesu al masihu,kuma ubangiji ya yarda da shi,suma zai yatda dasu, . saboda haka ,ba fushi yake dasu ba, yana fushi da laifin ne.

KU KARANTA : Pastor Bayan Masoyiyarshi Ta Mutu Gurin Zubda Ciki

An gano cewan mamban cocin da aka bulale, ya loda kaya shirye da shan bulala. Ashe!!! Fakewa da guzuma ake,a harbi karsana.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel