Dalibi ya kera jirgin sama mai tashin angulu a Najeriya

Dalibi ya kera jirgin sama mai tashin angulu a Najeriya

Wani lamarin da afku a kwana kwanan nan da wani dalibi dan Najeriya ya kera jirgin sama mai tashin angulu ya nuna cewa yan Najeriya mutane masu fasaha.

Dalibi ya kera jirgin sama mai tashin angulu a Najeriya
Mubarak a cikin jirginsa

Dalibin mai suna Mubarak Abdullahi dan asalin jihar Kaduna ya kera jirgin sama mai tashin angulu a gidansu. A cewar APC TV da ta bayyana labarin a shafinta na fcebook ta ce jirgin zai iya tashi sama nisan kafa bakwai, wanda hakan ya bada mamaki.

Dalibi ya kera jirgin sama mai tashin angulu a Najeriya
Dalibi ya kera jirgin sama mai tashin angulu a Najeriya

Mubarak dan shekara 25 ya kera jirgin ne da karafan alminiyam da injin motar Honda, da kingin wata mota kirar Toyota, da kuma kingin jirgi Boeing 747, sai dai ba’a tantance ko dama can Abdullahi na da ilimin kimiyya da fasaha ba. Amm dai duk da haka ya cancanci yabo.

Wannan nasaran da Abdullahi ya samu ya dara wanda Paul Onah ya samu wanda shima ya kera jirgin sama mai tahsin angulu ta hanyar amfani da wasu kanann kayan aiki. Hakan yaja hankalin Legit.ng inda muka yi mamakin yadda mutumin da bai je makaranta ba ya iya kera jirgin sama. Labarin da muka samu a yanzu na nuna mana cewa har anyi ma jirgin fenti. Abin da kawai ya rage ma Onah dan asalin jihar Benue shine ya samu kwarewa don ganin jirgin ya tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel