An damke mai kaima Boko Haram man fetur

An damke mai kaima Boko Haram man fetur

  Dan Boko Haram din ya musanta cewa ba shi ke kai mai ba

– Bincike ya nuna cewa, akwai yiwuwan cewa ya kai ma yan Boko Haram kayayyaki.

– Kakakin dakarun sojoji ya kara da cewa an haramta saye da siyar da man fetur a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

An damke mai kaima Boko Haram man fetur

Dakarun Sojojin Najeriya na cigaba da nuna jajircewansu akan yaki da ta'addanci a ranan talata ,19 ga watan yuli,yayinda suka damke asalin mai kaima yan Boko Haram man fetur. Yin bayanin wannan, Kakakin dakarun Sojin Najeriya, Kanal Sani Kukasheka, ya ce an kama dan Boko Haram din ne da jarkokin mai guda 25 da wasu kayayaki da aka boye a wurin duban mutane.

“Dakarun karakatfi ta 251 batallion,7 div gar sun kama wata mota lode da jarkokin man fetur 25 da wasu kayayyaki Wadanda aka boye a wajen duban Molai, wajen Maiduguri misalin karfe 8:00 na safe. Direban motan, Muhammadu Adamu yace bai saji abubuwan da ke ciki ba kuma ya kira mai motan,tijjani gambo yayi bayani. Shi ma Tijjani ya musanta kaiwa yan ta'adda man fetur da kaya ,kana yace shi dan kasuwane da ke kaiwa yan kasuwa kaya a damboa.  Amma, bincike ya juna cewa ya dade yana kaiwa yan Boko haram man fetur da wasu kayayyaki ta hanyar a lokaci baya lokaci kuma ba a samu wanda yace yana sayar mawa ba a damboa. Duk da cewa bincike na cigaba da gudana, ana zargin cewa ta wannan kafa ake kaiwa yan boko haram kayayyaki dajin sambisa, Kukasheka ya bada jawabi.

An damke mai kaima Boko Haram man fetur
An damke mai kaima Boko Haram man fetur

Ya sanar da cewa ai an haramta saya da sayen ,tafiye tafiye da man fetur a yankin. An tura abubuwan zargin da mahukuntan zuwa cibiyar bincike.

A wata labari mai kama da haka, a tsinta wata gawa a gidan man ruwan zafI dake gaban Gidan man NNPC, a hanyar Mafa-Dakwa. Marigayin mai suna  Aminu dan shekara kimanin 35-40,ya bar mata 1 da yara 4. “An daba mai wuka ne a kirjin sa . an kai karan faruwan ofishin yan sanda da ke jere domin gudanar da bincike, kuma ankai gawar dakin ajiye gawawwakin asibitib koyon jami'ar Maiduguri”. Ya kara

KU KARANTA : Kalli yadda sojojin Najeriya sukesa riguna da ganyayyaki

Ku tuna cewa a ranar litinin ,18,ga watan yuli,an kashe yan kungiyar Boko Haram 7 kuma sojoji 4 sunji rauni a batakashin da akayi . Kanal Usman yace dakarun sojojin 7 Division Strike Group Team B (7 DSGB), jingine da 21 Brigade, da 4 Civilian JTF ne suka share ragowan yan boko haram da ke Warpaya, Zenteleye, Mubarka, Jadawa da Yerwa .

Asali: Legit.ng

Online view pixel