Kocin Man City, Pep Guardiola ya sayo sabon gola

Kocin Man City, Pep Guardiola ya sayo sabon gola

 

– Kungiyar Manchester City ta saye wani sabon gola kan kudi fam miliyan 4 (Na Euro)

– Gola Rulli yana buga kwallo ne a La-liga ta Kasar Spain

– Sai dai dan wasan cikin ragar mai shekaru 24 zai koma Kasar ta Spain din aro.

Kocin Man City, Pep Guardiola ya sayo sabon gola

 

 

 

 

 

Pep Guardiola na Manchester City ya sayo wani sabon dan wasa; wane dan wasan mai tsaron raga, dan Kasar Argentina mai suna Geronimo Rulli. An dai saye gola Rulli din ne daga Kungiyar Deportivo Maldonado ta Kasar Uruguay. Dan wasan dai yana buga kwallo ne a Kasar Spain, inda ya lashe shekaru biyun da suka wuce a matsayin dan wasan aro a Kungiyar Real Socieded. Pep Guardiola ya samu sayen dan wasan akan kudi fam miliyan £4. Wani hanzari, ba gudu ba, dan wasan zai wakilci Kasar sa ta Argentina a Gasar Olympics da za a buga watan gobe a Brazil. Bayan nan kuma Golan zai sake komawa Kungiyar sa ta Real Sociedad da ke Spain ya cigaba a matsayin dan wasan aro daga Manchester City.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

Rulli Geronimo tun wuri ya nuna cewa ba zai iya kalubalantar Golan Kungiyar Manchester City da ma Kasar Ingila, Joe Hart ba a cikin raga. Saboda haka zai sake komawa Kungiyar sa ta Real Sociedad domin ya kara samun kwarewa. Hakan na nufin Willy Caballero zai cigaba da zama a Kungiyar Manchester City ta Ingila zuwa wata shekarar. Willy Caballero dai ya nuna gwaninta a bara, inda ya jagoranci kungiyar ta dauki kofin Capital One Cup a Watan Fabrairu, tsakanin su da Kungiyar Liverpool.

KU KARANTA: JUVENTUS NA NEMAN DAN WASAN NAPOLI.

Pep Guardiola dai yana neman wanda za su kara da Joe Hart a ragar Manchester City, bayan da dan wasan da ke tsaron ragar ya sha ciya-ciyai wajen Wales da Iceland a Gasar EURO da aka buga kwanan nan a Kasar Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel