Ambassador Tabari ya rasu a hadarin mota

Ambassador Tabari ya rasu a hadarin mota

– An tabbatar da cewan Ambassador tabari ya rasu a hadarin mota a hanyar Kaduna-Zaria

–   Wani makusancin iyalin marigayin , Alhaji Abdurrahman Nuhu-Bayero ya sanar da rasuwan a Zaria

– Za’a yi jana’izar sa a gidansu a rimin-kambari a zaria mislin karfe 2 na rana

Ambassador Tabari ya rasu a hadarin mota

 

Ambassador yahaya tabari,tsohon jakadan Najeriya zuwa kasar Afrika ta tsakiya ya rau a daren ranan litinin .18 ga watan yuli, sanadiyar wata hadarin mota Tabari ya rasu a hadarin mota ne a babban hanyar Kaduna zuwa Zaria, hukumar yada labarai ta bada rahoto.

Wani makusancin iyalin marigayin , Alhaji Abdurrahman Nuhu-Bayero ya sanar da cewan yahaya tabari ya rasu da shekara 64. Nuhu bayero yace yaha ya tabari yayi aikin da harokokin wajen najeruya a kasashe da dama wanda ya kunshi kasar Saudiyya, kasar Benin,kasar Afrika ta tsakiya.

KU KARANTA : Buhari ya shahara da yaki da rashawa – Jakadan Faransa

Ya kara da cewa za’a yi jana’izar sa a gidansu a Rimin-Kambari a Zaria. Ya rasu ne ya bar mata daya,hajiya binta da yara  5. Rasuwan Ambassador Tabari ya zo ne bayan rasuwam karamin ministan kwadago, Barrista James Ocholi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel