Dalilin dayasa Samuel Chukwueze bazai je Arsenal ba

Dalilin dayasa Samuel Chukwueze bazai je Arsenal ba

   - Samuel Chukwueze bazai je Arsenal ba.                              

   -Haka Kuma Kelechi Nwakali zaije kungiyar ta Gunners.           

   -Chukwueze dai yana daya daga cikin yan wasa masu hazaka a Flying Eagles. 

     Ana sa ran dai Samuel Chukwueze tare da Kelechi Nwakali zasu je kungiyar ta Arsenal, amman daga baya Kuma abun bai yiwu ba. Dan wasan dai yana cikin yan wasan Golden Eaglets wanda suka buga wasan duniya nayan kasa da shekaru 17 a kasar Chile a shekarar 2015 wanda ya basu daman daukan kofi.

Dalilin dayasa Samuel Chukwueze bazai je Arsenal ba
Kelechi Nwakali da Victor Osimhen

 

Majiyar sirrin da muka samu, Samuel Chukwueze bazai je Arsenal ba, saboda yana taya dan wasan kasa da abunda kungiyar tasa take nema.

A cewar majiyar, Chukwueze dan wasa ne mai hazaka wanda zai iya zuwa kungiyar ta Arsenal, to amman saidai yadda kocin Arsenal din yake taya dan wasan bai kai kudin da kulob din nasa suke bukata ba.

Sai dai ana tsammanin abokin dan wasan da suke buga wasa a Flying Eagles Kelechi Nwakali zai rattafama kungiyar ta Arsenal hannu a wata mai zuwa. Ana kuma tsammanin Gunners din zata kawo dan kasa da shekaru 20 din dan asalin Najeriya amatsayin aro.

KU KARANTA : Abunda Ahmed Musa yace game da Vardy

Nwakali wanda ya cika shekara 18 a watan daya gabata, zai sama Arsenal din hannu harna tsawon shekara biyar. Nwakali da Chukwueze suna cikin yan wasa Najeriya yan kasa da shekaru 20, wanda ana saran kungiyar ta Flying Eagles zata samu daman zuwa gasar AFCON na shekara mai zuwa.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel