Buri na in zama kamar Kanu Nwankwo-Ahmed Musa

Buri na in zama kamar Kanu Nwankwo-Ahmed Musa

LABARIN WASANNI

Buri na in zama kamar gwarzo, Kanu Nwankwo-Ahmed Musa

– Dan wasan gaba na Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana muradin sa na ya zama gwarzo a Premier League ta Ingila kamar tsohon dan wasa Kanu Nwankwo

–  Ahmed Musa yace ba a taba shahararren dan wasan Najeriya a Ingila ba kamar Kanu, ya kece su Jay Jay Okocha fa Finidi George.

– Ashe Ahmed Musa, tsohon mai tsaron raga (gola) ne a da.

Sabon dan wasan Leicester City, Ahmed Musa na Najeriya yace yana son ya ga ya ajiye tarihi a Ingila kamar tsohon dan wasa kuma abokin sa, Kanu Nwankwo. Dan wasa Ahmed Musa ya koma Kungiyar Leicester daga CSKA Moscow ta Russia kwanan nan, ya bayyana yadda yayi magana da Kanu kafin komawa kulob din Leicester, wanda su ka ci kofin Premier a bara. Ahmed Musa na kokarin bin sahun tsohon dan wasan gaban Najeriya, Kanu Nwankwo.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

Buri na in zama kamar Kanu Nwankwo-Ahmed Musa

 

 

 

 

 

 

Ahmed Musa yake cewa: “Za nayi iyaka bakin kokari na in zama kamar Kanu, Yan kasar Najeriya na kaunar buga kwallo a nan (Ingila), ina mai tabbacin cewa zan ji dadin kwallo a nan. Sai da nemi shawarar babban aboki na Kanu kafin in zo wannan kasa da kuma Kulob na Leicester. Kanu ya mani bayani, kuma ya bani shawarar in koma Ingila, za na ji dadi” Ahmed Musa yake tuna ma jama’a cewa: “Kanu yaci gasar Premier League a Kungiyar Arsenal, haka kuma ya ci FA cup bas au daya ba ma, da Arsenal da kuma Portsmouth.” Ahmed Musa yace: “Ba a taba samun dan wasa ba kamar Kanu (daga Najeriya). Ya zarce su Austin Jay Jay Okocha da su Finidi George”

Dan wasan ya kuma ba da labarin yadda har iso wannan mataki na yanzu, ya bayyana a baya can, mutane na ganin ba zai iya kwallo ba har ya zama mai buda zare (watau dan wasan gaba), akan ce da shi yayi kankanta. Yau ga shi a Ingila, ko can ya fada masu abin ba a girman jiki bane. A da can lokacin Ahmed Musa na shekara 12, tsaron gida ya keyi (watau gola), da abin ya faskara sai kuma ya koma rusa gidan (Watau dan wasan gaba). Dan wasan dai ya komo Kungiyar Leicester ta Ingila a ranar Juma’a 8 ga wannan wata.

KU KARANTA: Dan wasa Ahmed Musa yayi magana game da J. Vardy

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel